✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ku ragargaza ‘yan bindigar da suka addabi Katsina – Sadique

Babban Hafsan Sojojin Sama na Najeriya Air Marshall Sadique Abubakar ya umarci dakarun rundunar su ci gaba da yin barin wuta ga ‘yan bindigar da…

Babban Hafsan Sojojin Sama na Najeriya Air Marshall Sadique Abubakar ya umarci dakarun rundunar su ci gaba da yin barin wuta ga ‘yan bindigar da su ka addabi jihar Katsina har sai sun ga bayansu.

Abubakar wanda ya bayyana hakan yayin wata ziyarar aiki ga dakarun rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ da ke sansanin sojin sama a Katsina ya ce dole su gano mafakar ‘yan bindigar tare da fatattakar su har sai yankin ya sami sa’ida.

A cewar sa, “Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da aikinmu ba har sai al’ummar wannan jihar sun koma gudanar da rayuwarsu kamar yadda su ka saba a baya ba tare da fargabar harin ‘yan bindiga ko masu garkuwa da mutane ba.

“Za mu tabbatar dakarunmu sun samu duk kayan aikin da suke bukata don ganin bayan ‘yan ta’addan, mun kuma tabbatar ba su kara samun mafaka ba”, inji Babban Hafsan Sojojin.

Ya kuma bukaci mazauna yankunan da su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da bayanan sirri da za su taimaka wajen tona asirin miyagun.

Sadique ya kuma ce matukar hakan ta samu to babu shakka za a kawo karshen ‘yan bindigar tun da dai su ma a cikin al’ummar suke rayuwa.

Ko a kwanakin nan dai an jiyo gwamnan jihar Aminu Bello Masari yana cewa babu sauran sasanci tsakaninsu da ‘yan bindigar sakamakon kin mutunta yarjejeniyar da tun farko suka sanya wa hannu da gwamnati.

Masari ya ce don haka gwamnatinsa ba ta da wani zabi da ya wuce ta ci gaba da yakarsu.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar wa jihar tasa isassun kayan aiki don kawo karshen matsalar baki daya.