Daily Trust Aminiya - Ku tasa kayar duk Sanatan da ya gaza —Lawan
Subscribe

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan

Ku tasa kayar duk Sanatan da ya gaza —Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya bukaci ’yan Najeriya kar su zabi duk dan majalisar da bai yi musu ba ko ya gundure su a zaben 2023.

Shugaban Majalisar Lawan ya soki masu kira da a soke Majalisar Dattawar bisa hujjar makudan kudaden da ake biyan sanatoci.

Ya ce sokewar za ta haifar da danniya, a don haka abin da ya fi shi ne ’yan Najeriya su yi amfani da zaben 2023 su tasa keyar ’yan majalisar da ba su gamsu da su ba.

Lawan ya shaida wa taron Ma’aikatan Gudanarwar Majalisar Tarayya da na Hukumar Ayyukan Majalisar cewa Majalisar ce ke daidaita al’amura ta hanya tabbatar da wakilinci ga kowane bangaren kasa.

Ya ce ita ce ke tabbatar da daidaito a wakilci sabanin Majalisar Wakilai inda jihohi da suka fi yawan al’umma suka fi samun yawan wakilai.

More Stories