✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ku yi hattara da ’yan damfara masu amfani da sunana –Shugaban NNPC

Shugaban Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kolo Kyari, ya ankarar da al’ummar kasar game da wasu ’yan damfara masu amfani da sunansa a…

Shugaban Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kolo Kyari, ya ankarar da al’ummar kasar game da wasu ’yan damfara masu amfani da sunansa a dandalin sada zumunta na Facebook.

Mele Kyari ya yi wannan gargadi cikin wani sakon ankaraswa da ya wallafa kan shafinsa na Twitter a ranar Alhamis.

Ya sanar cewa akwai mazambata da suka bude shafuka akalla 25 a dandalin sada zumunta na Facebook da sunansa domin su damfari mutane.

A dalilin haka Kyari ya ke kira ga daukacin al’ummar Najeriya masu bibiyar zaurukan sada zumunta da su yi hattara domin gudun fada wa hannun miyagu.

Ya ce shi tun a shekarar 2015 ya daina amfani da shafin sada zumunta na Facebook.