✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kudin makamai: Kotu ta soke daurin da aka yi wa Olisa Metuh

Kotun Daukaka Kara ta ba da umarnin a saka sauraron shari'ar zargin cin kudin makamai

Kotun Daukaka Kara ta soke dauri da aka yi wa tsohon Kakakin Jam’iyyar PDP na Kasa, Cif Olisa Metuh.

Alkalan Kotun sun soke hukucin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Olisa Metuh a shari’ar zarginsa da cin kudin makamai.

Alkalan sun kuma umarci a sake sauraron shari’ar bayan a watan Fabrairun 2020 Mai Shari’a Okon Abang ya yanke wa Metuh hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari.

A shari’ar ta baya Kotun ta ci Metuh tarar Naira miliyan 375 da zai biya Gwamnatin Tarayya sannan ta umarci EFCC ta rufe kamfaninsa, Destra, Investment Limited.

EFCC ta gurfanar da shi ne bisa zargin karbar Naira miliyan 400 daga tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Kanar Sambo Dasuki, wanda aka karkatar zuwa yakin neman zaben tsohon Shugaban Kasa, Goodluck a 2015.