✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kullin kudirin kululun kiyayya

Sani-Attan Sababi Yai kullin kudirin kinbibi Ya baje a cikin babi Majalisar tsofaffi na ta bi Tai bita bi-da-bi   Mamakon murnar murmushin Marisa Dubun…

Sani-Attan Sababi

Yai kullin kudirin kinbibi

Ya baje a cikin babi

Majalisar tsofaffi na ta bi

Tai bita bi-da-bi

 

Mamakon murnar murmushin Marisa

Dubun karamin laujen Madambaci

Taga-tagar kudirin kaikayin hukunci

Kissar kisisinar kisa ba sassauci

Noman-Baban bana aka tisa

 

Tande-tanden tanderun toye-toye

Tandar tuyar tunkudo tawaye

Takadammar tada-komadar titsiye

Tutsun turnukun tambaye-tambaye

Taitayin takun tafiye-tafiye

 

Tatsuniyar gizo da koki

Jarumi na haifar da tarnaki

Batunsa ba fari da baki

Maganganun motsa makaki

Matakan takun shurin masaki

 

Kin kaya

Kaikayin kiyayya

Karajin karya

Kurjin kujewar kamuya-muya

Kasaitar kiriniya

 

’Yan majalisar dukan doka

’Yan jagaliyar daki-in-daka

Kaurayen babbaka

Taraliyar turka-turka

Mai ja wa uwarsa zagi ne dan kuka

 

Kudirin kayatar kura

Kundunbalar karkaro kara

Kankambar kurarin kira

Zabarin zaro zabira

Ce-ce-ku-cen cakwaikwaiwar carin cara

 

Laluben logar lankwasa lamura

Jajircewar jimirin jaruman Jajira

Tunkahon tambele tabara

Kwawazon kwarmaton katobara

Moruwar murmurewar mura

 

Cikin mutanen gari

Akwai nagargarun zahiri

Akwai miyagun magabta kiri-kiri

Ku zabi abin so da wuri

Ko da mugun da ya jefaku garari

 

Dokar dakushe kin magabci

Da kara soyayyar mamugunci

Da azzalumi macuci

Hada da makirai masu batanci

Har da shakiyan da ke iskanci

 

Samarin-kusu

’Yan matan jaba da gafiya

Beran dunka na tafiya

In sun yi kalami ban da musu

Ko watsa musu kasa sui bususu

 

Ai musu diskon duhu

Su washe damin matsabbai buhu-buhu

Suna ta hura iskar huhuhu

Sun wawushe taro da ahu

Sun maishe da kowa huhun-ma’ahu

 

Ni dai ba ruwana

Ka da doka ta hau kaina

Kar a ce na nuna karantsana

Mu ta fi kiwon karsana

Kafin su wawushe mini karfanfana

 

Cikin watan Marisar shekara ta dubu karamin lauje da sili da madambaci, Sani-Attan Sababi ya gabatar wa Majalisar tsofaffin Haurobiya kudirin kunduge karairayin kaskancin karfafa kin kayar  kurjin kululun karambon kiyayya. Wannan kudiri ya dan yi kundumbalar karkarewa a bara, amma cikin watan Noman-Baba na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar kasa sai lamarin ya yi wuntsila gudi-gudi ya wuntsilo da dirar da’irar dama-damar damuwar majalisa. Yanzu ana ta ka-ce-na-ce a ko’ina cikin fadin kasar nan, musamman ma jin cewa da zarar kudirin ya samu shallakewa da kutsawa cikin jerangiyar amintattun dokoki, tabbas duk wanda ya dura ashariyar aika-aikar aikin assha ga gunduma-gunduman garadan gudumar hukuma, to akwai yiwuwar a tabbar masa da hukuncin rataya. Kai kullin kudiri ya zo da kissar kisisinar kisa ba sassauci, amma dai an ce Malam Sababi ya dan sassauto, inda ya jajirce kan lallai sai kudirinsa ya samu shiga, ta yadda daga bisani a ciccire bukatar hukuncin halaka ga duk mutumin da kalamansa suka yi wa kasurguman mutane muni.

Bisa wannan dalili ya zama wajibi mu nusar da Haurobiyawa yadda za su tsahirta da kakarin kalallame kalaman kame-kamen SUKA-DA-BURTSATSEN MAGANGANU, ta yadda mahankalta za su magantu ko da an cika su da surutu rututu. Domin wannan batu na kudirin kumajin kankame kululun kurjin karambon kin kayar karairayin kiyayya kamuya-muya ce kawai da balulluba aka bullo da su don toshe bakunan al’umma daga suka mai ma’ana. Duk da cewa mun yi hannun taguwa da kudirin Malam Sababi, amma ni ma ban yarda da dura ashariyar ashararancin assha-assha ga kowane irin mutum ba, musamman idan ba shi ne ya auno gundun-gundun  ta uwa, ta uba, irin wannan yanayi sai kawai mu dauka so ake a keta masa haddi. Ni ma bisa wannan ina ganin zan iya jefa wa mutum SASARIN DAN MARI, af ashe an hana.

Karajin kamarin kululun karambon kin kayar kiyayya ta zaburar da ’yan majalisar kasar Haurobiya suka yi kundumbalar gabatar da kudirin karajin kurar karfafa soyayyar ’YAN MATAN JABA DA GAFIYA da BERAN-DUNKA, wadanda ya kamata mu sake musu kyakkyawan suna don gudun kada a ce mun yi kalaman aibata masu cutar da al’umma. Daga yanzu ba tare da babatun bata lokaci ba, sunansu ’YAN MATAN JIBGIN JIBA DA

GAFTARAR TIYA da BAMBARMAR DUKAN DOKA.

’Yan makaranta na sanku da bin doka, don haka ko IRO MUGUN MADAMBACI ne ya tabbatar da cewa wane da wane sun wawushe lalilitar kasar nan koda wasa kada inji ko in ga wanda zai aibata irin wannan mutumin; koda ma an fasko shi kiri da muzu yana daure dami. Domin kara bata sunan wanda aika-aikatarsa ta yi muni kalaman bata mutunci ne. Abin da ya sanya na yi wannan yunkuri cikin hanzari, shi ne, don ankarar da zakakuran ’yan makarantarmu yadda za su kauce wa auka wa komar  Kudirin kamarin kumajin karajin kululun karambon kin kayar karairayin kakaba kiyayyar kaka-kara-kaka. Saboda wannan lamari mai daure kurungu tamau ya zamo zantukan zarar ziryar zabarin make-maken Malam Makau mai makalutun makalo murmushin Marisar Mantau, tare da kin kakaba wa kurungu TUNTUN TAGIYAR TUNAU. Kun ga ke nan ba a tauna ba, sai kawai aka furzar. Don haka dole ne a irin wannan yanayi a ji motsin maskin makaki, ta yiwu ma a karke da magagi.

Haurobiyawa, ina ganin kundin kudirin kurungun kunduge kiren karairayin kululun kurjin karambon kiyayyar kaka-kara-kaka, tamfar tatsuniyar gizo da koki ce, domin sanin kowa ne gizo ya sha cutar da koki, tare da raina mata hankali. Kai akwai lokacin da gizo ya ce wa matarsa koki ta soya masa gyada “TA-SOYU” shi kuwa gwarzon gwarazan ya je ya daura shillo, ya yi ta lilawa, yana tauna marau-arau da kwankwadar na kwadi cikin nunin ninkayar nishadi. Kuma asirinsa ya tonu ne lokacin da aka zo girbi, inda ya je gayaunar Nomau Na-manomi ya dan rika yin halin bera, har suka yi karon-battar kar-ta-san-kar da arangama da budurwar danko.

Saboda haka dai in an ce a tatsuniyar gizo da koki jarumin juya akalar dokoki ya haifar da tarnaki, don batunsa babu bambance fari da baki, illa dai maganganun motsa muka-mukin makakin matakan tunkarar takun shurin masaki, ta yadda za a shagala da kumajin kadondoniyar kin kayar kaikayin kiyayyar karajin karairayin kurjin kullin kudirin kulle-kullen kujewar kamuya-muyar kasaitar kiriniya.

To in dai irin wannan tasuniyar ce sai mu ce ‘ta zo mu jita,’ da zarar an kai karshen tatsuniya kuwa, kowa zai ji an ce kurungus kan dan kusu ba don gizo ba, ai da na shara kiren karyar karairayi. Ko dai an sharata?

’Yan makarantar Dodorido mahaya shorido, ni dai ba ruwana ka da doka ta hau kaina har a fake da cewa na nuna wa wani karantsana, kamata ya yi kawai mu ta fi kiwon karsana, tun  kafin a wawushe mana karfanfana. Watakila dai saboda sun fasko cewa an yasar da kiwon bisashe, yanzu dan Adam ake yi wa tarairayar  kai-kawon kiwo, sai suka bullo wa Haurobiyawa da DABARBARUN DAMFARAR DAMUN-FURA ko?