✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kullum da matsalar tsaron Najeriya nake kwana – Buhari

Ya ce shi da jami'an tsaro kullum a cikin damuwa suke

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce kullum da matsalar tsaron da ta addabi Najeriya yake kwana yake tashi.

Ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa ga ’yan Najeriya albarkacin bikin Ranar Dimokuradiyya ta bana a ranar Lahadi.

Yayin da yake ba ’yan Najeriya tabbacin cewar gwamnatinsa na aiki ba dare ba rana wajen magance matsalar, ya hore su da su dada jajircewa da addu’o’i.

Buhari ya ce, “A wannan rana ta musamman, ina son dukkanmu mu sanya wadanda ayyukan ta’addanci suka shafa a cikin addu’o’inmu. Kullum da takaicin matsalar nake kwanan nake tashi.

“Ni da jami’an tsaro muna iyakar kokarinmu wajen ganin mun kubutar da mutanen da ’yan bindiga suka kama cikin aminci.

“Ga wadanda suka rasa rayukansu, za mu ci gaba da kokarin ganin mun kwato musu hakkokinsu a hannun wadanda suka zalunce su. Wadanda kuma yanzu haka suke a tsare, ba za mu rintsa ba har sai mun ga sun kubuta. Muddin muka hada kai, to ba shakka za mu yi nasara a kan wadannan miyagun masu shirin ganin bayanmu.

“Mun yi gyara a harkar tsaro. Wasu daga cikin kayan yakin da muka saya shekara uku da suka gabata yanzu sun iso, kuma an fara aiki da su.

“Mun bunkasa hanyoyin fasahar zamani don bin sahun wadannan bata-garin. Za kuma mu debi sabbin ma’aikata tare da horar da su a cikin dukkan hukumomin tsaro da na leken asiri don mu inganta sha’anin tsaron kasa,” inji Buhari.