✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kullum sai ’yan bindiga sun sace mana ’yan uwa —Mutanen Giwa

A kwana 10 mahara sun sace mutum 54 a kauyukan Karamar Hukumar Giwa

’Yan bindiga sun mayar da yankunan Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna wajen cin karensu babu babbaka kusan a kowace rana.

A yayin da mutanen yankin ke kokarin girbe amfanin gonarsu ganin cewa kaka ta yi, yankin na neman zama sansanin masu satar mutane don karbar kudin fansa.

Mutanen Giwa sun shaida wa Aminiya cewa tun daga farkon watan Oktoba zuwa yanzu kusan kullum sai ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a yankunansu.

Sun bayyana cewa a cikin kwana 1o da suka gabata ’yan bindiga sun sace akalla mutum 54 a kauyukansu.

Yankin ya jima yana fama da matsalar ’yan fashin daji masu kashe mutane, yin garkuwa da su da kuma satar shanu.

Aminiya ta gano cewa mafiya yawan gonakin yakin ba a sami damar noma su ba a daminar bana saboda yawaitar hare-haren ’yan bindiga.

Mahara sun hana mazauna noma

Duk da kokarin gwamnati da kuma nasarar jami’an tsaro a baya-bayan nan, har yanzu wasu yankunan na fama da matsalar rashin tsaro.

Mazauna yankunan sun shaida wa Aminiya cewa tun daga farkon watan har zuwa yanzu kusan kullum sai ’yan bindiga sun yi awon gaba da mutane a karamar hukumar.

Majiyoyin da suka nemi a sakaya sunayensu sun bayyana cewa sun rasa yadda za su yi saboda rashin noma gonakinsu tunda ba su da wata sana’ar da suka dogara da ita sai noma da kiwo.

Kazalika, rashin tsaro ya hana su yin noman, ga kuma tsadar kayan noma da ta rayuwa, don haka ba su da abin yi face su koma ga Allah domin neman sauki.

Wuraren da aka kai wa hari a Giwa

Mutanen yankin Giwa sun bayyana wa Aminiya cewa daga ranar 10 zuwa 21 na watan Oktoba, ’yan bindiga sun sace mutum 54.

Unguwar Sarki Dako

A ranar 10 ga Oktoba na wannan shekarar, ’yan bindiga sun kai hari kauyen Unguwar Sarki Dako da ke gundumar Yakawada da misalin karfe 10.30 na dare, suka yi awon gaba da mutane uku.

Majiyar Aminiya ta ce mutanen da aka dauke sun hada da Haruna Shuaibu da Kamala Abdulkarim da kuma Mamuda Haruna.

Unguwar Kawo

Majiyar ’yan sa-kai ta shaida wa Aminiya cewa a ranar da misalin karfe 11.30 na dare, maharan sun zarce zuwa kauyen Unguwar Kawo da ke gundumar ta Yakawada suka dauke mutane 15.

Sai dai majiyar ta ce sakamakon ba-ta-kashi da aka yi tsakanin maharan da ’yan sa-kai, an sami nasarar kwato mutane 5 cikin wadanda aka dauke.

Guguwa

A ranar 12 ga watan Oktoba kuma, ’yan bindiga sun kutsa kauyen Guguwa a Gundumar Kakangi da misalin karfe 1 na dare inda suka yi awon gaba da mata guda biyu, Saude Musa da Amina Musa.

Madarar Sarki

A ranar 18 ga watan Oktoba, mahara sun kai farmaki kauyen Madarar Sarki a Gundumar Gangara da misalin karfe 12.30 na dare suka yi awon gaba da mutane biyar.

Mutanen da aka sace su ne: Abu Abubakar, Amira Abubakar, Hasana Andurawus, Usaina Andurawus Mamman, Maijidda Barnabas da Basira Barnabas.

Garin Bako

Majiyar Aminiya ta kara da cewa a ranar kuma ’yan bindiga sun kai hari Garin Bako a Gundumar Kakangi da misalin karfe 1.15 na dare suka tafi da mutane shida.

Unguwar Mai Bakko

A ranar 21 ga watan Oktoba kuma suka shiga kauyen Unguwar Mai Bakko a Gundumar Yakawada suka yi awon gaba da mutane 10.

Sai kuma kauyen Unguwar Kasa Nature a Gundumar Yakawada inda maharan suka kwashe mutane 13.

’Yan bindiga ba su tare a Giwa ba —’Yan sanda

Da wakilin mu ya tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna, Mohammed Jalinge, ya ce, ya bayyana masa cewa, “Shi lamarin tsaro a kananan hukomomi 23 na Jihar Kaduna, an sami masara, kuma ’yan ta’addan ba wai tarewa suka yi a canba, a’a.

“Daga watan 4 har zuwa watan 10 na wannan shekarar mun kama ’yan ta’addan kusan su 11 tare da masu kai musu bayanai da kuma babura da makamai da dama.

“Dan haka ka ga ai an sami nasara, ba kamar a baya ba,” in ji ASP Jalige.