✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiya KYC ta karrama wasu fitattun mutane

Kungiyar Matasan Kaura (KYC) da ke Karamar Hukumar Kaura a Jihar Kaduna ta karrama wadansu fitattun mutum 20 saboda  gudunmawar da suka bayar a fannoni…

Kungiyar Matasan Kaura (KYC) da ke Karamar Hukumar Kaura a Jihar Kaduna ta karrama wadansu fitattun mutum 20 saboda  gudunmawar da suka bayar a fannoni daban-daban na ci gaban yankin.

Yayin da yake bayani a wajen bikin liyafar da aka gudanar a garin Kagoro da ke karamar hukumar, Shugaban Kungiyar KYC, Mista Derek Christopher ya ce sun yanke shawarar karrama mutanen ne don nuna farin cikinsu ga sadaukarwar da suka yi wajen ci gaban yankin musamman ta fuskar zamantakewa da siyasa da tattalin arzikin yankin da jihar da kasa baki daya.

Ya ce daya daga cikin wadanda suka karrama, Rabaran Bagayang Nwaya, sun karrama shi ne bisa ga jajircewarsa da kasancewarsa malamin addinin Kirista na farko dan asalin Kagoro kuma daya daga cikin kashin bayan kafa Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da na mutanen tsakiyar Najeriya (Middle Belt Forum) kuma daya daga cikin fitattun ’yan siyasa daga kananan kabilun Arewa mabiya addinin Kirista wanda ya assasa Kungiyar ‘Kagoro Peoples Progressibe Union’ da sauran ayyuka masu yawa. Sai ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta duba yiwuwar sanya wa wasu fitattun wurare sunansa don raya ambatonsa.

Baya ga shi, an karrama Shugaban Karamar Hukumar Kaura, Dokta Katuka Bege Ayuba, saboda gudanar da ayyukan raya kasa da ya yi a matsayinsa na shugaban riko wanda ba dan asalin karamar hukumar ba.

Christopher, ya bayyana Shugaban Karamar Hukumar a matsayin shugaba abin koyi wanda ba ya nuna son kai ko wariya ga jama’ar karamar hukumar.

Sauran wadanda aka karrama sun hada da Babban Jami’in Gudanarwa na Cibiyar ‘Cedar Seed Foundation’, Mista Louis Auta, wanda ya mayar da hankali wajen kyautata wa nakasassu da Mista Obadiah Sankyai, wanda yake taimaka wa jama’ar karamar hukumar.

Yayin da yake maida jawabi a madadin wadanda aka karrama, Mista Benjamin Bagayang, wanda Kwamishina a Hukumar Kula da Ma’aikata ta Jihar Kaduna, ya yaba wa wannan yunkuri inda ya bayyana farin cikinsa da zakulo ire-irensu da aka lissafa a matsayin wadanda suka taimaka wa wadansu.

Ya tabbatar wa kungiyar cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun dora daga inda suka tsaya wajen kyautata wa al’umma.