✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiya ta raba wa ’yan firamare 5,000 kayan abinci a Kafanchan

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Unic Foundation (SUWA) ta raba wa daliban makarantun firamare 5,000 kayayyakin abinci da suka hada da danyar shinkafa…

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Unic Foundation (SUWA) ta raba wa daliban makarantun firamare 5,000 kayayyakin abinci da suka hada da danyar shinkafa da wake da kuma magi.

Da yake jawabi wajen taron da aka gudanar a sabon filin wasan kwallon kafa na garin Kafanchan hedkwatar Karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna, Shugaban Kungiyar SUWA ta Kasa, Mista Christopher Imumolen, ya ce hakan na daga cikin yunkurinsu na taimaka wa harkar ilimi wajen ganin ya tafi daidai da kudirin bunkasa ilimi da Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya a gaba.

Ya ce wannan yunkuri zai taimaka wa iyaye wajen rage musu kashe kudi a harkar ilimin ’ya’yansu.

“Muna da niyyar fadada ayyukanmu,  musamman ganin yadda aka karbe mu hannu bibbiyu tare da yaba wa wannan aiki namu, saboda ganin fa’idarsa don haka muke fatar samun goyon bayan da musamman daga wadanda suka ci gajiyar shirinmu,” inji shi.

A jawabin shugaban yanki na gidauniyar, Samson Oteikwu, ya ce cibiyar ta tsara ayyuka masu yawa da take shirin gudanarwa don taimaka wa ’ya’yan marasa galihu a fannin ilimi, kuma sun tuntubi dukkan cibiyoyi a fadin jihar domin tattara adadin mutane da irin abin da suke bukata  a tallafa musu da shi.

“Daga cikin shirye-shiryenmu akwai tallafin sukolashif da za mu bai wa dalibai a makarantun firamare da sakandare da tallafa wa mata da jarin gudanar da manya da kanana da matsakaitan sana’o’i da koyar da sana’o’i da kuma taimaka wa manoma da marasa lafiya,” inji shi.

Ko’odinetan Kungiyar ta Kasa, Emmanuel Idiale, ya ce manufarsu ita ce su kawar da talauci a fadin kasar nan ta hanyar bayar da tallafin kudi da harkokin kasuwanci da cinikayya.

Mai martaba Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammad Isa Muhammad, wanda Sarkin Gandun Jama’a, Alhaji Suleiman Isa ya wakikta, ya jinjina wa kungiyar bisa ga tallafa wa dalibai da sauran mabukata a masarautarsa don ganin ci gaban yankin da kuma kokarin tabbatar da manufar kungiyar.

Malamai da daliban makarantun gwamnati da na masu zaman kansu da iyayen yara da wakilan sarakunan gargajiya suka halarci taron.