✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kungiya za ta aurar da zawarawa 700 a Kaduna

Wata kungiya mai zaman kanta a Kaduna za ta aurar da zawarawa 700 da kuma tallafa musu da jari.

Wata kungiya mai zaman kanta a Kaduna ta kammala shirye-shiryen daukar nauyin aurar da zawarawa 700 da kuma tallafa musu da jari.

Kungiyar mai suna Gidauniyar Sardaunan Badarawa tana sa ran zawarawan da za su ci gajiyar za su fito ne daga Kananan Hukumomin Kaduna ta Tsakiya.

Wanda ya kirkiri kungiyar kuma Sardunan Badarawa, Alhaji Usman Ibrahim ya ce rukunin farko na auren zai kunshi zawarawa masu karamin karfi ne da suke bukatar yin aure.

Ya ce za a zabo a kuma tantance zawarawa 100 daga kowacce Karamar Hukuma a Kaduna ta Tsakiyar sannan kuma a basu tallafin jari bayan yin auren.

Sardaunan na Badarawa ya kara da cewa za su hada kai da shugabannin addini da masu rike da sarautun gargajiya wajen shirya bukukuwan auren.