✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Ansaru ta nesanta kanta da harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Bayanan maharan sun nuna kusnacinsu da kungiyar Darul Salam, inji dan jarida mai binciken kwakwaf

Kungiyar Ansaru ta nesanta kanta harin da aka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna aka kashe fasinja tara, aka kuma yi garkuwa da wasu 62 a watan Maris.

Kungiyar ta musanta zargin da ake mata na hannu a harin ne ta wasu takardu da ta rika raba wa matafiya a kan Babbar Hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua.

Takardun da kungiyar ta raba sun nuna cewa manufar Ansaru ita ce kare Musuluncui daga abin da ta kira, “Zaluncin gwamnatin Najeriya da sauran kasashen Afirka bakar fata.”

Wani shugaban matasa a yankin Birnin Gwari da ya bukaci a boye sunansa ya ce ’yan kungiyar sun yi ta raba takardun ne ga matafiya da sauran matane a kan babbar hanyar a ranar Alhamis da yamma.

“Babu wanda suka kai wa hari, kawai dai suna ta raba wa direbobin motocin haya ne takardun a kan babbar hanyar Birnin Gwari,” inji shi.

Takardun sun ce babu ruwan akidar kungiyar da kai wa mutane da ba su ji ba, ba su gani ba hari — babbar manufarta ita ce kare addinin Islama da Musulumi da aka zalunta ko aka ha’inta.

Kungiyar ta kuma karyata wani mai suna Abu Barra da da ke ikirarin cewa shi ne shugabanta, inda ta ce nan gaba za ta sanar da shugabanta.

Tun a ranar 17 ga watan Afrilu wani shafin Facebook da ake zargin na dan kungiyar Ansaru ne, ya karyata rahotannin da ke alakanta kungiyar da harin da aka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris, 2022.

Kazalika, dan jarida mai binciken kwakwaf kan matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce da wuya idan kungiyar na da hannu a harin da aka kai wa jirign kasan.

“Maganar da suka yi na ’ya’yansu da aka kama a Nasarawa da kuma uslubin maganarsu da aka nada ta waya, sun nuna maharan sun fi kusanci da ’yan kungiyar Darul Salam, amma ba kungiyar Ansaru ko Boko Haram ba,” a cewarsa.