✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Dalibai za ta shiga zanga-zanga kan yajin aikin ASUU

ASUU da gwamnatin su gaggauta kawo karshen tankiyar da ke tsakaninsu.

Kungiyar Dalibai ta Najeriya NANS ta caccaki Gwamnatin Tarayya hadi da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU kan abin da ta kira gazawar bangarorin biyu na warware takaddamar da ke tsakaninsu.

Cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar NANS na kasa, Asefon Sunday Adedayo ya fitar a ranar Litinin, ya ce muddin gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU ba su kawo karshen tankiyar da ke tsakaninsu ba, to kuwa babu abin da zai yi ma su shamaki da gudanar da zanga-zanga a fadin kasar nan don ganin malaman jami’ar sun yayyafawa zukatansu ruwan sanyi sun koma aji.

A jawabin da Mista Sunday ya yi kan yajin aikin gargadi da kungiyar ASUU ta tsunduma, ya bayyana cewa halin ko in kula ne ya janyo an kasa samun maslaha tsakanin bangarorin biyu ba tare da an rufe jami’o’i da tsayar da karatun dalibai ba.

A safiyar Litinin da ta gabata ce ASUU ta sanar da cewa ta tsuduma yajin aikin gargadi na mako hudu inda ta zargi gwamnatin tarayya da gazawa a cika alkawuran da ta yi wa kungiyar.

Da yake yi wa manema labarai jawabai bayan kammala taron Majalisar Zartarwa na kungiyar a Jihar Legas, Shugaban ASUU na kasa ya ce kungiyar ta yi iya yinta don ganin ba ta dauki wannan hukunci na shiga yajin aiki ba, amma gwamnatin tarayya ta gaza ba da muhimmancin da ya kamata ga batun biyan bukatun mambobinta.

Aminiya ta ruwaito cewa, ASUU ta cimma matsayar fara yajin aiki kai tsaye domin tilastawa gwamnatin kasar biya mata bukatun ta tare da cika yarjejeniyar da suka kulla tsawon shekaru da suka gabata ciki har da shekara ta 2011.

Rahotanni sun yi nuni da cewa a yayin zaman taron Majalisar Zartarwar kungiyar, ASUU ta yanke shawarar tsunduma cikin yajin aikin na gargadi ne da zimmar ba gwamnatin kasar kafar sauke nauyin da ya rataya a wuyanta tare kuma da gargadin cewa muddin gwamnati ta gaza biya mata bukatunta, ASUU dai zata shiga yajin aikin na gama-gari.