✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar kwadago ta ki amince wa da karin farashin man fetur

Ba za ta sabu ba domin kuwa hakan ya saba wa yarjejeniyar da muka kulla da Gwamnati.

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, ta sauka daga matakin kurum din da ta yi, inda a Yammacin Litinin ta yi martani kan wutar da ’yan Najeriya suka huro mata dangane da karin farashin man fetur zuwa Naira 170 duk lita da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Gamayyar kungiyoyin kwadagon da suka hada da NLC da ta ’yan kasuwa TUC, sun hau kujerar naki ta amince wa da karin farashin litar man fetur tare da cewa ba za ta sabu ba domin kuwa hakan ya saba wa yarjejeniyar da ta kulla da Gwamnatin Tarayya.

Shugaban NLC Ayyuba Wabba cikin wata sanarwa da ya fitar yayin zanta wa da manema labarai, ya ce kungiyarsu ta kwadago ta yi Allah-wadai da karin farashin litar man fetur tare da cewa hakan babu abin da zai haifar face kara jefa al’ummar kasar cikin mayuwacin hali bayan wanda suke cikinsa.

A cewar Wabba, karin farashin litar man fetur da aka yi kwanan nan ya ci karo da yarjejeniyar da kungiyar kwadago ta kulla da Gwamnatin Tarayya a zaman sasancin da ta yi da ita bayan karin farashin man fetur da ta yi a baya.

Shugaban kungiyar ya ce wannan rashin dattako da Gwamnatin Tarayya ta nuna na rashin tsaya wa a kan magana daya zai zubar da mutuncin kungiyar tare da janyo mata nakasun kima a idanun ’yan Najeriya.