✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar mata ta jinjina wa gwamnatin Yobe kan dokar hana cin zarafin mata

Kungiyar t ce dokokin za su kawo karshen cin zarafin matan

Wata Kungiyar sa-kai ta mata mai zaman kanta a Jihar Yobe, ta jinjina wa Gwamnan Jihar Mai Mala Buni, game da tura dokar hana cin zarafin mata da kananan yara ga Majalisar Dokokin Jihar.

Shugabar kungiyar, Barista Altine Ibrahim, wacce ta yi jinjinar ta ce dokokin za su hana cin zarafi da nuna kyama da kuma tozarta su tare da goyon bayan wasu gamayyar kungiyoyin na sa-kai.

Barista Altine, ta ce lallai hakan ya tabbatar da cewa tsarin Gwamnatin Jihar zai tabbatar da kare ’yancin mata.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Magatakardar kungiyar, Hajiya Fatima Paga, da aka raba wa manema labarai a garin Damaturu, babban birnin Jihar.

Kungiyar ta kuma ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su tabbatar da sanya wa dokar hannu.

A cewarta, kungiyarsu za ta ci gaba da bai wa gwamnati hadin kai da goyon baya tare da sauran kungiyoyin da suke hulda don ganin an tabbatar da shigar da jinsi cikin al’amuran ci gaba na gwamnati, a matakin Jiha da ma kasa baki daya.