✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kungiyar MULAN ta Kasa ta yi taro a Jigawa

An bukaci ’ya’yan Kungiyar Lauyoyi Musulmi, (MULAN), su rika yin shigar kayan aikin lauya domin su bi tsarin dokar aikinsu na lauya. Shugaban Kungiyar Lauyoyi…

An bukaci ’ya’yan Kungiyar Lauyoyi Musulmi, (MULAN), su rika yin shigar kayan aikin lauya domin su bi tsarin dokar aikinsu na lauya. Shugaban Kungiyar Lauyoyi Musulmi ta Kasa (MULAN) Farfesa Adeleke ne ya yi kiran a wajen taron kungiyar na kasa da aka yi a Dutse a ranar Asabar da ta gabata. Ya shawarci ’ya’yan kungiyar su rika shigarsu ta lauyoyi maimakon su saka doguwar riga ko manyan kaya, domin hakan ya yi daidai da tsarin aikinsu – wanda ya tanadi shiga ta musamman; ta yadda duk wanda ya gan su zai gane su cikin sauki.

Shugaban ya yi kukan karancin kudi da ya ce ya  addabi kungiyar, lura da ginin katafariyar sakatariyarsu ta kasa da suka fara a Abuja ba su kammala ba, lamarin da ya sanya a nan take a wurin taron aka bude asusun neman taimako, inda aka tara kudi sama da Naira miliyan daya da rabi.

Farfesa Adeleke, ya bukaci ’ya’yan kungiyar a duk inda suke da su taimaka wa kungiyar da duk abin da za su iya don ganin aikin da suka sa a gaba an kammala shi.

Ya ce nan da wani lokaci kadan suna sa ran kammala aikin ginin sakatariyar da sauran kananan aikace-aikacen da suka rage a kammala a sakatariyarsu da ke Abuja

A jawabin,tsohon Kwamishinan Shari’a na Jihar Jigawa Malam Tijjani Inuwa Dutse, ya hori ’ya’yan kungiyar su rika bada gudunmawarsu duk wata a rika cirewa daga albashinsu da nufin agaza wa kungiyar.

Tsohon Kwamishinan Shari’a na Jihar Barista Sani Husaini Garun Gabas ya bada gudunmawar Naira dubu 500.

Reshen kungiyar na Jihar Kaduna ya bayar da Naira dubu 650 yayin da shiyyar Abuja ta bada Naira dubu 500; sai kuma wadansu daidaiku da suka bayar da tasu gudunmawar.