✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Musulmai ta nemi sauya lokacin kidaya saboda azumi

Wata kungiyar Musulmai mai suna Islamic Forum ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sauya lokacin fara kidaya na 2023, saboda ya zo a…

Wata kungiyar Musulmai mai suna Islamic Forum ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sauya lokacin fara kidaya na 2023, saboda ya zo a lokacin da Musulmai ke azumin watan Ramadan.

Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar dauke da sa hannun Babban Sakatarentana kasa, Farfesa Salisu Shehu, ya ce kwanan watan da aka sanya na 29 ga Maris zuwa 1 ga watan Afrilu, ya yi daidai da lokacin da Musulmi ke azumin Ramadan.

A cewar sanarwar, “Ban da wahalar rashin takardun kudi da ake fama da su, akwai abubuwa da dama, ciki har da tafiye-tafiye zuwa wasu yankunan da ba na Musulmi ba da ke nesa da mahaifarka.”

Haka kuma ya ce tura Musulmi wadannan wuraren, zai sanya su yi asarar sallolin Ashan da na Tarawi, hadi da Tafsiri, da buda baki da sahur.

Don haka kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin da ta duba kimanin Musulmi miliyan 120 da su ne ake sa ran za su yi azumin na bana a Najeriya ta sauya lokacin zuwa wanda ba zai takura wa kowa ba, kamar bayan Sallah.