✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kungiyar NAAT ta dakatar da yajin aikinta na gama gari

Sai dai sun ce ba su amince da 'ba aiki, ba albashi ba'

Kungiyar Ma’ikatan Fasahar da ke a Jami’o’in Najeriya (NAAT) ta dakatar da yajin aikin da take yi na tsawon wata biyar a fadin kasa, amma ta ce ba ta amince da tsarin ‘ba aiki, ba albashi’ ba.

Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Ibeji Nwokoma ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan taron Majalisar Zartarwa ta Kasa na kungiyar a Abuja ranar Alhamis.

Nwokoma ya ce, Kungiyar NAAT ta shiga yajin aikin ne a ranar 21 ga watan Maris, 2022, don matsa wa gwamnati ta biya bukatunta da suka hada da: rashin cika yarjejeniyarsu da ita ta 2009, da kin fitar da takardar da ke ba da damar aiwatar da CONTISS 14 da 15 ga masana fasahar ilimi da rashin biyan basussukan kudaden alawus-alawus na Ilimi ga mambobinsu da sauransu.

Ya ce daukar matakin kungiyar ya biyo bayan cim ma matsaya da gwamnati kan wasu bukatunta, duk da cewa ta ki amincewa da tsarin Gwamnatin Tarayya na ‘Ba aiki, babu albashi’.

“Bayan wannan fahimtar da gwamnati ta yi, kungiyar NAAT a matsayin kungiyar dimokuradiyya, ta umurci dukkan rassanta da su gudanar da zaben jin ra’ayi kan ko za a dakatar da yajin aikin ko a’a.

Majalisar Zartaswa ta Kasa ta NAAT ta yi taro tare da duba sakamakon rassan ne dai a ranar Alhamis, 25 ga watan Agustan 2022.

Sakamakon kuri’ar raba gardama daga rassan kungiyar ya nuna cewa kaso 80.56 cikin 100 na mambobin nata sun amince da dakatar da yajin aikin, yayin da kaso 19.44 cikin 100 suka kada kuri’ar ci gaba da shi.