✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Tajdid ta yi karar Gwamnatin Kano kan Sheikh Abduljabbar

Mazhabar ta ce idan gwamnati ta kasa gurfanar da Abduljabbar a kotu, ta kauce ta ba su wuri.

Kungiyar Jammaatu Tajadid Islamy (JTI), ta yi karar Gwamnatin Kano da Kwamishinan ’Yan Sanda Jihar tana neman a gaggauta hukunta Sheik Abduljabar Nasiru Kabara wanda ake zargi da cin zarafin Annabi Muhammad (SAW).

Kungiyar mabiya mazhabar na neman kotun ta umarci Babban Lauyan Jihar Kano Barista M. A Lawan da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Samaila Dikko, su gaggauta kame Abduljabar su gurfanar da shi.

Amma kungiyar ta Tajdid na ikirarin cewa girman laifin da ake zargin Abduljabar da aikatawa ya wuce Gwamnatin Jihar Kano ta yanke hukunci a kai ita kadai.

A takardar karar da lauyan JTI, Barista Abubakar Tanko ya karanta, ta ce Abduljabar ya aikata babban laifi da Babbar Kotu ce kadai za ta iya wanke shi.

“Muna tuhumar Sheik Abduljabar Nasiru Kabara da aikata manyan laifuka karkashin dokar hukunta laifuka ta shekarar 2020, wanda a fili ta ayyana hukuncin aikata batanci.

“Muna sane cewa Gwamnatin Jiha ba ta da iko a doka ta dakatar ko ta tsoma baki a batun zargin batanci har sai Kotun da ta dace ta yanke hukunci”.

Barista Tanko ya ce idan har Jiha ba za ta iya gurfanar da Sheik Abduljabar a gaban kuliya ba to ta kyale Mazhabar ta gurfanar da shi yadda ya kamata kamar yadda dokar kasa ta 2000 ta tanada.

Idan ba a manta ba wata kotun majistare a Kano ta dakatar da mukabalar da aka shirya gudanarwa tsakanin Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara da malaman Kano.