✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kungiyoyi sun koka kan jinkirin shari’ar Zakzaky

Gamayyar kungiyoyin farar hula karkashin jagorancin wata kungiya mai fafutukar kawo ci gaba da tabbatar kare hakkin dan Adam a Najeriya sun yi kira ga…

Gamayyar kungiyoyin farar hula karkashin jagorancin wata kungiya mai fafutukar kawo ci gaba da tabbatar kare hakkin dan Adam a Najeriya sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hukunta masu hannu wajen ci gaba da tsare mabiya akidar Shi’a da sauran kananan kungiyoyi a Najeriya ba bisa ka’ida ba.

Kungiyoyin sun ce hakan zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da adalci da ci gaban kasa.

Kungiyoyin sun bayyana haka ne a wata sanarwar hadin gwiwa mai dauke da sa hannun Dakta Hasan Bala, Geoffrey Nwokolo, Prince Adelaje Adeoye, Comrade Ecoja Godwin, Dakta Y. B. Abubakar, Kwamared Ahmad Shuaib da kuma Kwamaret Mabel Christiana Abba.

Sun yi kira da a gaggauta gurfanar da wadanda suka yi abin da suka kira ‘kisan kiyashin’ da aka yi wa mabiya Shi’a domin su girbi abin da suka shuka.

Kungiyoyin sun yi zargin take hakkin ‘yan Shi’a mabiya jagorancin Shaikh Ibrahim Zakzaky wanda hakan kuma ya kai ga kashe-kashe da kuma tsarewa ba bisa ka’ida ba.

“Wadannan laifukan da aka aikata kan tsirarun ‘yan Shi’a abu ne dab a za mu taba mantawa ba a fafutukarmu ta tabbatar da kare hakkin dan Adam a cikin mulkin dimukradiyya.

“Cin zarafin da aka yi wa ‘yan kungiyar marasa rinjaye, jagoransu Zakzaky da matarsa Zeenat tare da ajiye su ba bisa ka’ida ba tsawon lokaci duk irin raunukan da suka ji saboda harsashen da aka harbe su da shi, watsi da umarnin babbar kotun Abuja na sakinsu tare da biyansu diyyar Naira miliyan 50 duk muna nan sane da su”, inji kungiyoyin.

Sun kuma yi kira da a gaggauta mika wadanda ke da hannu a cin zarafin ‘Yan Shi’ar ga Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya (ICC) bisa aikata laifukan yaki tare da kisan kiyashi.