✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kurewar wa’adin Saudiyya: Zargin cuwa-cuwar biza ya dabaibaye NAHCON

Ana zargin jami'an Hukumar Aikin Hajji da Cefanar da biza, ejen kuma sun tsawwala farashi har ya kai Naira miliyan daya.

’Yan sa’o’i kafin cikar wa’adin da Saudiyya ta ba wa Najeriya ta kammala jigilar maniyyatan aikin Hajji, matsaloli sun kara dabaibaye jigilar maniyatan a Najeriya.

Wasu maniyata da jami’an hukumomin jin dadlin alhazai na jihohi na zargin Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da bin bayan fage wajen neman biza, wana hakan ya sa aka sako bizar maniyyata da dama.

Maniyyatan na zargin wa jami’an NAHCON da cuwa-cuwa ta hanyar cefanar da bizar maniyyata, musamman ga masu bin jirgin yawo.

Fusatattun maniyyatan daga jihohi na kuma caccakar kamfanonin jiragen da hukumar ta ba wa jigilar alhazai a bana, saboda gazawa wajen kwashe maniyyata a kan lokaci.

Zuwa ranar Talata dai NAHCON ta ce maniyata 29,128 da ma’aikata 920 ne suka isa Kasa Mai Tsarkin, kuma bizar maniyyata 8,620 da za su bi jirgin yawo sun kammalu.

Maniyyatan da za su zauna a gida

Hakan ya jefa maniyyata kimanin 5,000 — tare da ma’aiakata — cikin zullumi game da yiwuwar zuwan su Hajji a bana.

Hukumomin jin dadin alhaza na jihohi da dama sun bayyana rashin gamsuwa bisa yadda NAHCON ta gaza sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.

Sun kuma dora wa hukumar laifin haddasa yawancin matsalolin da suka dabaibaye aikin Hajjin a wannan karon.

Aminiya dai ta gano cewa maniyata 1,120 ne daga cikin 2,265 daga Jihar Neja ba su samu tafiya Hajjin ba ya zuwa yammacin ranar Talata.

A Jihar Bauchi kuwa, an sanar da maniyyata 150 da suka rage a sansanin alhazai cewa su koma gida su hakura, saboda ba za su samu bisa ba.

Akalla maniyyata da ma’aikata 100 ne a Jihar Kaduna ake tunanin ba za su samu zuwa aikin Hajji ba.

Maniyyata 60 kuma daga Jihar Filato ba za su samu tafiya ba.

Zuwa ranar Talata dai maniyyta 1,300 daga Jihar Kano ne ba su tafi Saudiyya ba, ko da yake hukumar jin dadin alhazan jihar ta ce tana kyautata zaton dukkansu za su sauke farali tunda kamfanin jirage na Flynas ya kawo musu dauki.

Cuwa-cuwar biza

Hakan ta ritsa da su ne saboda NAHCON ta kasa sama musu biza a kan lokaci, duk da cewa sun riga sun biya kudadensu.

Wani maniyyaci a Jihar Bauchi ya ce ejen-ejen sun tsawalla farashin biza, har suna karbar Naira dubu dari bakwai.

Ya ce wasu ma har Naira miliyan daya suka rika karba kudin biza a makon da ya gabata.

Amma a zantawarsa da Aminiya, Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris, ya ce ba shi da wata masaniya cewa NAHCON na maye gurbin bizar maniyyatan jihar.

Takwaransa na Jihar Filato kuwa, Auwal Abdullahi, ya ce bai san dalilin rashin samuwar bizar maniyyata 60 daga jikin 278 da suka rage a jihar da aka riga aka kai su filin jirgi na Bauchi, inda za su tashi ta nan zuwa Saudiyya ba.

Aminiya ta gano cewa yawancin wadanda haka ta shafa maniyyata ne da gwamnatin jihar ta dauki nauyinsu, ciki har da jami’an gwamanti.

Kokarin wakilanmu na jin ta bakin mai magana da yawon NAHCON, Fatima Usara, ya ci tura.

Mun kira ta domin jin daga bangaren hukumar, amma har muka kammala hada wannan rahoto ba ba ta samu amsa kiran namu ba.