✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kuri’a ce kadai ke ba da damar zaben wanda ake so —Gwamnan Gombe

Da katin zabe ne kadai mutum zai iya zabar wanda ya kwanta masa a rai.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya yi kira ga al’ummar jihar da su fito a dama da su a aikin sabunta katin zabe da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fara gudanarwa.

Gwamnan ya yi kiran ne a lokacin da yake wa dumbin magoya bayan jam’iyyarsu ta APC jawabi a Makarantar Firamare ta Jekadafari da ke jihar wadda ita ce cibiyar tattara sakamakon zabe na gundumar.

  1. ’Yan bindiga sun kashe mutum 18 a Kaduna
  2. PDP da APC Danjuma ne da Danjummai —Jega

“Kuri’a ce kadai hanya daya tilo da za ta bai wa mutum damar zaben shugaban da ya kwanta masa a rai,” a cewar gwamnan.

Aminiya ta ruwaito cewa, Gwamnan ya kasance a cibiyar tattara sakamakon zaben ne domin tabbatar da ba samu wata tangarda ba wajen bayyana sakamakon zaben gundumomi da aka gudanar na jam’iyyar APC.

Ya yi amfani da wannan damar wajen rokon mambobin jam’iyyar APC da su mance da duk wani banbance-banbance da ke tsakaninsu domin sake tabbatar da nasarar jam’iyyar a 2023.

Kazalika, ya taya wadanda suka samu nasarar zama sabbin shugabanni murna, inda ya shawarce su zamo adalai tare da riko da gaskiya.

Alhaji Usman Aliyu Ashaka, shugaban Karamar Hukumar Gombe, ya yaba wa gwamna kan yadda ya samar da kyakkyawan yanayi da ya bada dama aka gudanar da zaben a dukkan mazabu yadda ya dace.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Shugaban Kwamitin Zaben, Dokta Danjuma Dabo ya ce nasarar zaben da aka samu na da nasaba ne da hadin kan da aka samu a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.

Haka kuma, Dabo ya ce salon tsarin jam’iyyar ne ya kawo musu wannan nasarar, inda har ya zuwa yanzu ba a su samu wani rahoto na korafi a kan zaben ba.