✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kuri’a Jin Ra’ayi: Ana zargin ba Biden ke Shugabancin Amurka ba

An bukaci Majalisar Tarayya ta bi diddigin wannan lamari cikin hanzari.

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a Amurka ta nuna cewa akasarin Amurkawa suna ganin ba Shugaban Kasar Joe Biden ne yake jagorantar gudanar da manufofin kasar ba.

Kashi 57 cikin 100 na wadanda suka kada kuri’ar da kungiyoyin Conbention State Action da Trafalgar Group suka suna ganin Shugaba Biden bai cika gudanar da ayyukan ofishinsa ba.

Yayin da kashi 36 suke da yakinin cewa Shugaba Biden ne yake jagorantar dukkan manufofi da batutuwan da suka shafi tafiyar da harkokin gwamnati.

Kashi 59 na wadanda suka jefa kuri’ar daga magoya bayan Jam’iyyar Democrat suna ganin ba Biden ne yake jan ragamar mulkin kasar ba. Sai kashi 32 daga cikinsu suka nuna kishiyar haka.

Kuma kashi 84 na masu jefa kuri’ar ’yan Jam’iyyar Republican, sun ce basu yarda Joe Biden ne yake gudanar da ayyukan ofishinsa ba.

Sai kashi 10 na masu jefa kuri’a daga magoya bayan Republican suka ce shi ne yake jagorantar dukkan manufofi da batutuwan da suka shafi tafiyar da harkokin shugabancin kasar.

Kashi 58 na wadanda suka jefa kuri’ar daga masu zaman kansu, sun ce ba su yarda cewa Biden ne yake gudanar da ayyukan shugabanci ba.

Yayin da kashi 36 na masu zaman kansu suka amince cewa shi ne yake tafiyar da kasar.

Kusan kashi 10 na ’yan Democrats da kashi biyar na ’yan Republican da kuma masu zaman kansu sun bayyana cewa ba su da tabbacin cewa “Biden ne yake jagorantar gwamnatin kasar.

“Sakamakon jefa kuri’ar ya tabbatar da cewa mutane sun cancanci sanin lafiyar Biden da lafiyar kwakwalwarsa, inji Mark Meckler, Shugaban Kungiyar Convention State Action.

“Mutanen Amurka sun cancanci sanin gaskiyar lamari game da gwamnatin Biden da kuma hakikanin halin da lafiyarsa take ciki.

“Sannan akwai bukatar shugabannin Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai su bi diddigin wannan lamari cikin hanzari.

“Watakila amsoshin da za su fito su kasance abin kunya ne ga tsarin dimokuradiyyarmu,” inji Meckler.

An gudanar da kur’iar jin ra’ayin ce a tsakanin 23 zuwa 25 ga Yunin bana.

Daga cikin mutum 1,086 da suka kada kuri’ar, an samu kuskuren kari ko ragi da kashi biyu da digo casa’in da bakwai.