✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kusan rabin kafafen yada labaran Afghanistan sun rufe harkokinsu – Bincike

Hakan dai ya sa kusan kaso 60 na ’yan jaridar kasar sun rasa ayyukansu.

Kusan rabin kafafen yada labarai a Afghanistan sun rufe harkokinsu tun bayan da kungiyar Taliban ta karbi mulkin kasar a watan Agustan 2021.

Wani bincike da Kungiyar Kare Hakkin ’Yan Jarida (RSF) da Kungiyar ’Yan Jarida ta Afghanistan (AIJA) suka gudanar, ya gano cewa kusan kaso 43 cikin 100 na kafafen sun kulle harkokinsu a kasar.

Hakan, a cewar binciken, ya jefa kusan kaso 60 cikin 100 na ’yan jaridar kasar cikin rashin aikin yi.

A cewar binciken, karbar mulkin na Taliban ya yi matukar shafar yadda suke gudanar da harkokinsu.

Daga cikin tashoshi 543 da ke watsa shirye-shirye a kasar a farkon shekarar 2021, ya zuwa karshen watan Nuwamba, 312 daga cikinsu ne kawai suke aiki. Daga cikin muhimman dalilan da suka jefa su cikin mawuyacin halin, akwai kalubalen tattalin arzikin da kasar ta fada da kuma kuma irin sabbin dokokin da Taliban ta kakaba musu.

Tun bayan kama mulkin kungiyar dai, mata ne lamarin ya fi shafa, inda kaso 82 cikinsu suka rasa aiki.

’Yan jarida dai a Afghanistan sun kasance cikin tsaka mai wuya cikin shekara 20 da suka gabata, inda kungiyoyin ISIS da Taliban da ’yan daba da ma gwamnatin Ashraf Ghani da kasashen Yamma suka mara wa baya, suka rika kai musu hari.

A shekarar 2018 kawai, an kashe ’yan jarida shida sannan aka raunata wasu da dama a wani harin kunar Bakin Wake wanda ISIS ta dauki alhakin kaiwa.