Kuskure ne ziyarar da Ganduje ya kai wa Garo —Kwamishina | Aminiya

Kuskure ne ziyarar da Ganduje ya kai wa Garo —Kwamishina

Dokta Muhammd Tahar Adam, Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar Kano
Dokta Muhammd Tahar Adam, Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar Kano
    Salim Umar Ibrahim, Kano da Abubakar Muhammad Usman
Kwamishina Harkokin Addini na Jihar Kano, Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible), ya ce ba daidai ba ne ziyarar da gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya kai wa Murtala Sule Garo.

Baba Impossible ya caccaki gwamnan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Kano, inda ya ce ziyarar da Ganduje ya kai wa tsohon kwamishinan nasa a matsayinsa na gwamna bai dace ba.

“Idan zabe ya matso, za ka ga abubuwa na tasowa saboda bukatar kai; Duk wanda bai samu abin da ya ke so ba, wasu za su ci gaba da zama wasu kuma za su fice zuwa wani wajen da za su ke ganin za su samu abin da suka je nema — ba sabon abu ba ne.

“A matsayinsa na gwamna, kafafen watsa labarai sun rawaito yadda ya je gidan mutumin da ya nada a matsayin dan takarar mataimakin gwamna da Sanata Barau.

“Ba daidai ba ne gwamna kamar shi ya ziyarci kwamishinan da ke karkashinsa; Zai iya kiran shi a duk lokacin da yake so.

“A matsayin uba yake, mahaifi yakan kira dansa ne ba wai ya je da kansa ba.

“Ko da ficewa zai yi daga jam’iyyar sai ya bar komai a hannun Allah, sai ya yi kokarin gyara inda ya san ya yi kuskure.

“Ba za mu ce babu inda ba a yi kuskure ba. Wannan gwamnati ce dole a samu kura-kurai.

“Ya je gidan Sanata Shekarau abin da ya faru bai yi dadi ba mutane sun masa ihu, kuma daga karshe abin da ya je domin sa bai samu ba, gaskiya ba mu ji dadi ba.
“Ta ya za mu gyara kura-kuranmu, mu hadu waje daya mu yi addu’a da neman mafita, ba wai mu tafi wajen wani muna ba shi hakuri ba.”

Aminiya ta rawaito yadda wani sabon rikici ya kunno kai cikin jam’iyyar APC a Jihar Kano, inda dan takarar mataimakin gwamnan Jihar, Murtala Sule Garo, ke shirin ficewa daga jam’iyyar.

Ana zargin rikicin ya kunno kai ne sakamakon sulhun da Ganduje ya yi da Sanata Barau Jibrin, babban abokin hamayyar Garo a yankin Kano ta Arewa.