✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kusoshin Taliban 6 da suka jagoranci kifar da gwamnatin Afghanistan

Ga wasu daga cikin kusoshin Taliban guda shida.

Kungiyar Taliban ta shafe shekara 20 tana fafatawa da gwamnatin kasar Afghanistan da ke samun goyon bayan kasashen Yamma tun shekarar 2001.

Taliban dai ta samo asali ne daga mayakan wata kungiya da ake kira ‘Mujahideen’  wadanda suka fatattaki mamayar dakarun rusasshiyar Tarayyar Soviet a shekarun 1980.

Kungiyar dai ta bulla ne a shekarar 1994 a matsayin daya daga cikin bangarorin da suka fafata yakin basasar kasar wacce daga bisani kuma ta karbe iko da mafi yawan sassan kasar a 1996, sannan ta kaddamar da Shari’ar Musulunci.

Abokan adawarta da ma kasashen Yamma da dama dai sun zargeta da cusa wa mutane tsarin Shari’ar Musulunci ba tare da son ransu ba, da kuma musgunawa mabiya wasu addinan mara sa rinjaye a kasar.

Wanda ya kirkiri kungiyar, Mullah Mohammad Omar daga bisani ya tsallake ya bar kasar bayan dakarun gwamnatin kasar da suka sami tallafin Amurka suka hambarar da gwamnatin Taliban a shekarar 2001.

A lokacin dai, saboda rashin sanin wurin da ya buya, hatta mutuwarsa sai bayan shekara biyu duniya ta sani ta bakin dansa.

Ga wasu daga cikin kusoshin Taliban guda shida:

Haibatullah Akhunzada

Wanda aka fi sani da ‘Amirul Muminin’ Haibatullah dai masanin Shari’ar Musulunci ne kuma shi yake da wuka da nama kan batutuwan kungiyar da suka shafi siyasa da addini da kuma harkokin soji.

Haibatullah Akhunzada
Hoto: Aljazeera

Ya karbi ragamar ne daga Akhtar Mansour wanda wani harin dakarun Amurka ya kashe a kan iyakar kasar da Afghanistan a 2016.

In ban da bacewarsa a 2016, Haibatullah ya shafe shekara 15 yana koyarwa tare da yin wa’azi a wani masallaci da ke garin Kuchlak da ke Kudu maso Yammacin Pakistan.

Shekarunsa 60 a duniya kuma har yanzu ba a san a inda yake ba.

Mullah Mohammad Yaqoob

Da ga wanda ya kirkiri kungiyar Taliban, Mullah Omar, Mullah Yaqoob dai shi yake kula da harkokin sojin kungiyar, kuma kafafen yada labaran kasar sun yi ittfakin yana cikin Afghanistan.

Mullah Mohammad Yaqoob
Mullah Mohammad Yaqoob

A baya dai, wasu da suka yi yunkurin ballewa daga kungiyar sun so su yi masa mubayi’a a matsayin jagora.

To sai dai shi kuma ya yi wa Haibatullah mubayi’a saboda ba shi da isasshiyar gogewa a bangaren yaki, sannan yana da karancin shekaru.

Yaqoob dai na tsakanin shekara 30 ne a duniya.

Sirajuddin Haqqani

Da ga fitaccen kwamandan kungiyar Mujahidin, Jalaluddin Haqqani, Sirajuddin dai shi ne ke kula da kadarorin kudi da na sojin kungiyar da ke tsakanin kan iyakar Afghanistan da Pakistan.

Ana dai tunanin cewa iyalansu ne suka kirkiro harin kunar bakin wake, kuma sune suka kitsa hare-hare da dama da suka yi sanadiyyar kisan manyan mutane a kasar, ciki har da wani mummunan hari da ya yi yunkurin hallaka Shugaban Kasar na wancan lokacin, Hamid Karzai da kuma wanda aka kai ofishin jakadancin kasar Indiya.

Sirajuddin Haqqani

Shekarunsa ba su wuce tsakanin 40 zuwa 50 ba, kuma ba a san a inda yake ba.

Mullah Abdul Ghani Baradar

Yana daya daga cikin wadanda suka kirkiri kungiyar, kuma a yanzu haka shi yake jagorantar ofishin siyasar Taliban, kuma yana daya daga cikin tawagar da ke tattaunawa a birnin Doha na kasar Qatar domin duba yuwuwar tsagaita wuta a kasar.

Mullah Abdul Ghani Baradar

Sai dai a ’yan watannin nan, hakar tattaunawar ta gaza cimma ruwa.

Rahotanni sun ce Abdul Ghani na daya daga cikin kwamandojin da Mullah Omar ya fi amincewa da su.

Jami’an tsaron Pakistan sun taba kama shi a birnin Karachi na kasar, amma daga bisani suka sake shi a 2018.

Sher Mohammad Abbas Stanikzai

Tsohon Mataimakin Minista ne a gwamnatin Taliban kafin a hambarar da ita, kuma ya shafe kusan shekara 10 a birnin Doha.

Shi ne zama jagoran ofishin siyasar kasar a shekarar 2015.

Sher Mohammad Abbas Stanikzai
Sher Mohammad Abbas Stanikzai

Ya kasance daga cikin wakilan Taliban da suka tattauna da gwamnatin Afghanistan kuma ya wakilci kungiyar a tarukan diflomasiyya a kasashe da dama.

Abdul Hakim Haqqani

Shi ne jagoran tawagar tattaunawa na kungiyar, tsohon Alkalin-alkalan kungiyar wanda ya jagoranci Majalisar Malamanta mai matukar tasiri.

Abdul HakimAbdul Hakim Haqqani Haqqani
Abdul Hakim Haqqani

Mutane da dama dai na ganinsa a matsayin wanda Haibatullah ya fi amincewa da shi.