✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kutsen Intanet: EFCC ta kama ’yan damfara 10 a Fatakwal

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki ta’annati a Najeriya, ta cafke wasu mutum 10 da ake zargi da aikata laifin kutse…

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki ta’annati a Najeriya, ta cafke wasu mutum 10 da ake zargi da aikata laifin kutse a yanar gizo a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.

Kakakin Hukumar reshen jihar Ribas, Wilson Uwujaren ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai cikin birnin Fatakwal a ranar Laraba.

Ya ce mutanen da aka cafke ana zarginsu da damfarar jama’a ta hanyar satar bayanai a yanar gizo domin wawusar kudi da kadarori.

“An cafke wadanda ake zargin ne a wani gida mai lamba 23 da ke lungun Sam Mba a unguwar God City da ke kusa ta titin NTA Akparale a birnin na Fatakawal.”

“An kama su ne bayan tattara bayanan sirrin da aka samu game da zarginsu da hannu a aikata zamba ta yanar gizo,” in ji shi.

Mista Uwujaren ya lissafo kayayyaki da aka samu a hannun ababen zargin da suka hada da motoci na alfarma guda uku, wayoyin salula 11, komfutar tafi da gidanka 4, katukan ATM da sauransu.

Kakakin hukumar ya ce za a gurfanar da ababen zargin a gaban kuliya da zarar sun kammala binciken da ake gudanarwa a kansu.