✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwace filaye: El-Rufai ya kalubalanci Kudancin Kaduna

El-Rufai ya caccaki sarakunan da ke cewa kwace filaye a Kudanci yankin ne ke kawo rikice-rikice

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya kalubalanci sarakunan Kudancin jihar su bayyana ko da taki daya na fili da aka yi kwacensa a yankinunansu.

Ek-Rufai ya kalubalance su ne a taron Majalisar Sarakunan Jihar, inda ya ce tun shekarar 2016 ake yayata zargin kwace filaye a yankin ba tare da kawo wata kwakkwarar hujja ba.

“Karairayin da ake dangantawa da rikicin a yanzu sun hada da zargin kisan kiyashi da kwace filaye, amma tun 2016 an kasa kawo shaida.

“Na ba wa duk wani basarake izini ya fada wa ‘yan jarida daidai da taki daya na kasa da wani ko wata kungiya ta kwace da karfi ko ta haramtacciyar hanya a yankinsa”, inji shi.

El-Rufai ya mayar da martanin ne saboda zargin da sarakunan yankin suka yi cewa kwace wa jama’ar yankin filayensu na da hannun a rikicin baya-bayan nan a yankin.

Gwamnan ya gaya wa taron cewa karairayin da ake bazawa game da halin da ake ciki a Kudancin jihar ba zai hana kokarinsa na kawo zaman lafiya a jihar da ke fama da rikice-rikice na tsawon lokaci.