✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwadayin kudi ke kai wasu ’yan kwallon Firimiyar Ingila —Kroos

Kungiyoyin Ingila sun kashe fam biliyan 1.9 wajen cefanen ’yan wasa a bana.

Dan wasan tsakiya na Real Madrid, Toni Kroos, ya kwance wa gasar Firimiyar Ingila da ’yan wasanta zani a kasuwa.

Kroos mai shekaru 32 ya ce galibi ’yan kwallo na koma wa kungiyoyin Firimiyar Ingilan ce saboda neman albashi mai tsoka a madadin neman samun nasarori a fagen sana’ar tamaula.

Wannan na zuwa ne a matsayin martani ga masu ruwa da tsaki na Firimiyar da ke ganin cewa gasar ce a sahu na gaba ta fuskar daukar hankali da kuma kwarewa.

Toni Kroos ya ce kungiyoyin Ingila ba sa wani abun zo a gani a manyan gasanni kamar Kofin Zakarun Turai duk da irin makudan kudi da kungiyoyin suke batarwa wajen sayen ’yan kwallo, musamman ma a kasuwar hada-hadar ’yan wasan ta bana da aka rufe a makon jiya.

A zantarwarsa da tashar OMR, Kroos ya ce, “kudaden da ake samu ta hanyar haska wasannin Firimiyar Ingila ya fi na kowace gasa a shekarun nan, amma hakan bai sa kungiyoyinsu sun iya lashe dukkanin gasannin da suke bugawa ba.

“Tabbas ba duk ’yan kwallon da ke buga wa a Ingila ne suka sa kwadayin albashin mai tsoka ba, domin akwai wadanda samun nasara da lashe kofuna da kuma kara kwarewa a fagen tamaula suka sa a gaba,” a cewarsa.

Kroos yana cikin ’yan kwallon da suka buga wa kungiyar Real Madrid a wasan karshe na Kofin Zakarun Turai da suka lallasa Liverpool a kakar da ta wuce, inda ya lashe kofin karo na biyar a tarihinsa.

Babu shakka dai kungiyoyin Firimiyar Ingila sun sake kafa tarihi a kasuwar hada-hadar ’yan kwallo da aka rufe kwanan nan, inda sun kashe kimanin fam biliyan 1.9 (£1.9bn) wajen cefanen ’yan wasa a bana.

Wannan ya nuna sun goge tarihin da suka kafa na kashe fam biliyan 1.4 (£1.4bn) wajen sayen ’yan wasa a 2017.

Alkaluma sun nuna kungiyoyin Ingila sun kashe kudi fiye da abin da aka kashe wajen sayen ’yan wasa a sauran manyan gasannin Turai da suka hada da La Liga ta Sfaniya da Serie A ta Italiya da kuma Bundesliga da ake bugawa a Jamus.