✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalara: Mutum 21 sun kamu, 2 sun mutu a Filato

Ma'aikatar Lafiyar Jihar ta bukaci jama'a da su kiyaye da matakan tsafta

Mutum 21 sun kamu da cutar kwalara yayin da wadansu biyu suka mutu sanadiyyar ta a Jihar Filato. 

Kwamishinan Lafiyar jihar, Dokta Nimkong Ndam, shi ne ya tabbatar da hakan a wata ganawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ranar Alhamis a Jos.

Ya ce an yi wa mutum 30 gwajin cutar inda aka gano 21 cikinsu na dauke da ita.

Sai dai ya ce tuni aka yi wa wadanda aka samu da cutar magani har ma an sallame su.

A cewar Kwamishinan, kwalara dai cuta ce mai sa tsannanin gudawa wacce kwayar cutar Vibro cholera ke haddasawa; galibi ana samun ta cikin ruwa ko abincin da bahaya da ya gurbata. 

Ya yi kira ga jama’a da su kasance suna wanke ’ya’yan itatuwa da ganyayyaki sosai tare da tafasa ruwan sha domin kashe kwayar cutar da ke haddasa kwalara. 

Ya kuma bukaci mutane su rungumi dabi’ar wanke hannu da amfani da man wanke hannu idan babu babu ruwan domin kauce wa yaduwar cutar.