✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalara ta kashe mutum 169 a Kano, 191 na kwance a asibiti

An yi kira da a kula da tsaftar abubuwan da ake ciki da kuma ta muhalli.

Gwamnatin Jihar Kano ta ce barkewar cutar Kwalara a Kananan Hukumomi 44 na jihar ta yi ajalin mutane 169, yayin da a halin wasu mutum 191 ke kwance a asibiti.

Daraktan Sashen Kula da Lafiyar Al’ummar na Ma’aikatar Lafiyar Jihar, Dokta Ashiru Rajab ya shaida hakan yayin ganawarsa da manema labarai a ranar Alhamis.

Dokta Rajab ya ce, an tattaro wannan alkaluma ne cikin watannin ukun da suka gabata kawo yanzu wanda a cewarsa mutum 5,221 suka kamu da cutar kuma daga ciki 4,860 sun samu sauki.

A cewarsa, mutum 191 da suka rage wadanda suka kamu cutar na kwance a asibitoci daban-daban da ke fadin jihar inda suke samun kulawa.

Yayin da yake da jaddada cewa suna duk wata mai yiwuwa domin ganin karshen lamarin, Dokta Rajab ya yi kira ga al’umma da su kula da tsaftar abubuwan da suke ciki da kuma ta zamantakewa musamman a yankunan karkara domin kare kai.

A bayan nan Aminiya ta ruwaito cewa, aka samu jimillar mutum 479 aka tabbatar da mutuwarsu sanadiyar barkewar cutar Kwalara a fadin kasar.