✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalara ta kashe mutum 20 wasu 200 na kwance a Binuwai

Mutum 200 sun kamu da annobar a kasa da sati uku bayan barkewarta a Jihar

Akalla mutum 20 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar amai da gudawa, a kananan hukumomi hudu da ke Jihar Binuwai.

Shugaban Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC), reshen jihar Ikechukwu Oradu, yace hakan ta faru ne tun bayan bullar cutar a ranar 10 ga Janairu, 2021.

Kananan hukumomin hudu da cutar ta barke sun ne Guma, Agatu, Gwer ta Yamma da kuma Makurdi.

Oradu, a yayin ziyararsa ga Mataimakin Gwamnan Jihar, Injiniya Benson Abounu, ya ce binciken NCDC ya nuna mutum 20 sun mutu wasu 200 kuma sun kamu da annobar.

Binciken, a cewarsa ya kuma gano cewar shan ruwa da abinci mara kyau ne suka haifar da bulla cutar.

Ya roki gwamnatin jihar da ta gina rijiyoyi da makewayi saboda dakile yawan yin bahaya a fili.

Da yake jawabi, Mataimakin Gwamnan ya ce Ma’aikatar Lafiyar Jihar ta shiga ceton rayukan wadanda suka kamu da cutar tun bayan bullarta.

Abounu ya kara da cewa gwamnatin jihar ta ba da umarnin gina katafaren dakin gwajin cutar COVID-19 da sauran cututtuka masu yaduwa a jihar.