✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalara ta kashe mutum 479 a Najeriya —NCDC

NCDC ta ce an samu karuwar masu kamuwa da cutar a Kano da wasu jihohi.

Cutar kwalara ta kashe akalla mutum 479 a jihohi 18 da aka samu bullarta a Najeriya a wannan shekarar.

Rahoton da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta fitar ya ce kawo yanzu  mutum 19,305  ne suka kamu da cutar a jihohin 18 da Birnin Tarayya.

“Daga farkon wannan shekara zuwa ranar 11 ga Yulin 2021, mutum 19,305 ne suka kamu da cutar, daga cikinsu 479 sun rasu a jihohi 18 da Birnin Tarayya.

“Kashi 11 cikin 100 da masu cutar kananan yara ne masu shekaru biyar zuwa 14. Kashi 52 cikin 100 na mutanen maza ne, sai mata kashi 48 cikin 100,” inji rahoton.

NCDC ta kara da cewa an samu karuwar masu kamuwa da cutar ta kwalara a jihohi hudu da suka hada da Kano da Bauchi da Jigawa da kuma Kwara.

Alkaluman da ta fitar sun nuna daga ranar 5 zuwa 11 ga watan Yuli mutum 31 ne cutar kwalara ta kashe a Najeriya.

Jihoin da aka samu bullarta su ne Kano da Kaduna da Zamfara da Gombe, da Bauchi da Jigawa da Nasarawa da Yobe da Binuwai.

Sauran su ne Kebbi da Kwara da Filato da Neja da Kogi da Delta Kuros Riba da Bayelsa da kuma Abuja.

Cutar kwalara tana iya kisa kuma an fi kamuwa da ita ne daga amfani da gurbataccen ruwa.

Alamominta sun hada da amai da gudawa da karancin ruwa a jika da rashin kuzari da ke iya haddasa jijjiga ko rauni a koda da sauransu.