✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalara ta kashe mutum 60 a Katsina

Yanzu haka gwamnati na raba maganin yaki da cutar kyauta a asibitoci.

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da mutuwar mutane 60 sakamakon barkewar cutar Kwalara a jihar wadda alkaluma suka nuna ta harbi fiye da mutane da 1,400.

Kwamishinan Lafiyar Jihar Yakubu Danja ya bayyana hakan yayin ganawa da Shugabannin Kungiyar Likitocin Najeriya a birnin Katsina.

“Muna sane da halin da ake ciki na barkewar Kwalara a wasu sassa na jihar nan.

“Yanzu haka muna da mutum 1,400 da suka kamu da cutar, yayin da mutum 60 kuma suka rasu.”

Danja ya ce yanzu haka gwamnatin na raba maganin yaki da cutar kyauta a asibitocin da ke jihar domin dakile yaduwar cutar, tare da kuma shelar yadda jama’a za su kare kan su daga harbuwa da ita.

A yayin da Kwamishinan ke gargadin mazauna jihar a kan tabbatar da tsaftar abinci da ruwan sha da kuma ta mahalli, ya ce ana ci gaba da kokarin dakile yaduwar cutar a dukkan Kananan Hukumomi 34 na jihar.

A makon jiya hukumomi a Jihohin Sakkwato suka sanar da mutuwar mutum 23 sakamakon harbuwa da cutar.

Haka kuma, a makon jiyan ne dai aka samu mutum 30 da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon cutar a Jihar Zamfara.