✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan uwa 5 sun rasu a garin jana’izar mai kwalara a Sakkwato

An kwantar da mutum biyar daga cikin ayarin da suka kamu da cutar a hanya.

Akalla mutum biyar ne ’yan uwan juna suka mutu a kan hanyarsu ta zuwa Sakkwato daga Jihar Legas, bayan daukar gawar dan uwansu wanda ya rasu sakamakon kamuwa da cutar kwalara.

Wadanda suka mutun masu aikin karfi ne da ke zuwa Jihar Legas yin aikin tono lokaci zuwa lokaci.

Aminiya ta gano suna cewa mutanen da bin ya ritsa da su suna zaune ne a Ijeota, yankin da cutar ta kwalara ta fi kamari a Jihar Legas.

Daya daga cikinsu ne ya fara kamuwa da cutar, kuma take ta kashe shi cikin dan kankanin lokaci.

“Bayan rasuwarsa sai ’yan uwan nasa suka yanke shawarar mayar da gawarsa zuwa garin Sanyinna da ke Karamar Hukumar Tambuwal a Jihar Sakkwato don yi masa jana’iza.

“Sun dauki hayar bas zuwa Sakkwato, a kan hanyarsu mutum biyar suka sake rasuwar bayan sun kamu da cutar kafinsu isa.

“Yanzu haka an kwantar da wasu mutum biyar daga cikin fasinjojin da suka kamu da cutar ta kwalarar a asibitin Sanyinna.

“Mun hana motar shiga garin, mun umarci direban da ya wuce kai tsaye zuwa asibiti kuma hakan ya yi lokacin da suka karaso,” a cewar wata majiya.

Ardon garin Sanyinna, Alhaji Shehu Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wadanda suka rasun sun baro Legas ne zuwa Sakkwato.

Ya kara da cewa an yi musu sutura tare da binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.