✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalin Digiri ba lasisin aiki ba ne: Ra’ayoyin masu karatu

A matsayinka na mai digiri a jami’a, za ka iya sayar da dankalin turawa?

A ranar Lahadi 19 ga watan Yuli  2020 ne Aminiya ta wallafa wani rahoto inda ta zanta da Faruk Rabilu Mai Dankali matashi dan shekara 27 da ke zaune a garin Jos, babban birnin Jihar Filato, wanda ya yi karatu har matakin digiri amma ya kama kasuwancin sayar da dankalin turawa, inda yake shiga kauyuka yana sayo dankalin, yana kawowa garin Jos ya sayar.

Aminiya ta wallafa tamabaya kamar haka:

A matsayinka na wanda ya yi karatun digiri a jami’a, za ka iya sayar da dankalin turawa?

Ga yadda mahawarar ta kasance:

Zaharaddeen Nasir: Ni yanzu haka wallahi aikin tura ruwa nake yi. Kuma da kwalin digiri dina a hannu tare da sakamako mai kyau (Second Class Lower). Na yi karatu a sashin kimiyyar na’urar mai kwakwalwa (Computer Science) a jami’ar jihar Sokoto.

Kada ka raina sana’a ko ya take saboda ya fi a dinga ganinka kofar gidajen ‘yan siyasa ko kana roko balle sana’a mai mutunci irinta dako, wadda aikin karfi ne.

Wani yana can da kwalin digiri da sakamako mafi kyau, amma ko gurin zuwa yin aikin dako ba ya dashi. Mu gode ma Allah a duk halin da ka tsinci kanka dan ka fi wani.

Ka dinga kallon na kasanka kada ka kalli na samanka. Allah Ya sa muda ce.

Murtala Naseer: ALHAMDULILLAH bisa dukkan alamu mun kama hanyar samun nasarori a rayuwarmu da kuma samun waraka daga illar da karatun Boko ya yi wa wannan al’ummartamu ta Hausa/Fulani ta fuskar watsi da ma kyamatar kananan sana’o’i’n da muka sami iyayenmu a kai saboda kawai mun je mun koyi karatu da rubutu da yaren wani.

Arziki na Allah ne, sannan rungumar kananan sana’o’i zai rage mana mugun buri da kuma kawazucin samun aikin gwamnati da shiga aikin da mummunar niyyar tara abin duniya ko ta halin kaka.

Ina rokon Allah Ya sa mana albarka a hanyar nemanmu, Ya kuma saukar mana da alheri mai yawa daga falalarsa.

Kawu Usman Zangina: Ko da digiri ko ba digiri duk sana’ar da take halacce, ai me hankali zai yi in ya samu. Abin kunya shi ne, a kama mutum ya saci kayan wani.

Abubakar Ahmad Rufa’i: Mi zai hana, ai wannan sana’a ce, kuma zuwa karatun digiri ba yana nufin na wuce kasuwanci dan neman na kaina ba. Komai zan iya in dai zan sami rufin asirin rayuwata wallahi.

Kabiru Suleiman: Me zai hana ya fi a ce mutum ya yi sata, kare mutunci ne.

Salis S Jibril:  Yanzu haka a iya unguwarmu wadanda suke da kwalin digiri sun fi a kirga su, banda irinmu da ba mu karasa ba kuma kar ka yi tunanin masu kwalin a hannu aiki ne da sufa a wasu wurare suna yin kananan sana’o’i.

Wasu kuma sun kashe zukatansu suna jiran gwamnati, yanzu ko ni yanzu karamar sana’a na dogara da’ita, kuma da hakan nake rike kaina kuma nake daukan nauyin karatuna, ina tukin babbar mota kuma wannan tukin bai hana ni karatuna ba.

Naziru Sani Sarauniya: Abin da ma bai kai sayar da dankalin turawa ba ma zan yi.

Amma ni shawarata ga matasanmu idan mun gama digiri a lokacin da muke yi wa kasa hidima, me zai hana mu yi amfani da kudin tallafin wata wato allowance din da gwamnati take ba mu mu dinga rage wani abu daga cikin wanda idan mun gama yi wa kasar hidima din mun koma gida wannan abun da muke ragewa sai mu fara yin sana’a da su mu dogara da kanmu kar mu bari zuciyarmu ta mutu da karbar dubu 33 a wata, ka ga shi karbar wannan kudin lokaci ne da shi.

Ina fatan ’yan uwana matasa za mu dauki wannan shawara tawa, na san idan muka dauke ta insha Allahu za mu yi nasara, fatanmu shi ne a kullum Allah Ya sa mu dace.

Muhammad Alhaji: Ina da kwalin digiri shekara 3 data wuce na gama da (Second Class Upper) amma yanzu haka ina sana’ar gini ne kuma da ita nake biya wa kaina bukatu da sauran makusantana.

Kuma ina neman aikin gwamnati ko zan dace amma ban dogara da digirina ba kuma ina fatan matasa su daina dogaro da ita saboda kowa Allah Ya yi masa hanyar cin abincinsa aiki na gwamnati a yanzu sai dan gidan masu hanya.

Yakub Yakub Ahmad: In Allah Ya rubuto min hakan to ya zan yi sai na rike kuma na nemi Allah Ya sa min albarka a kan sana’ar tawa.

Mahmud Auwal Bunkure: Mene ne amfanin kwalin digiri a Najeriyarmu ta yanzu? Abin da bai kai wannan ba ma zan yi shi, domin na rufa wa kaina asiri!

Salman Skd Ahmad: Ban ga abin girman kai a nan ba da ma don me mutum ya yi karatun? Don ya iya tafiyar da rayuwar cikin sauki.

Nazifi Abdullhi: Kai da guduma na gama A B Y amma tarugu nake sayarwa.

Aminullah Abubakar Abdullahi: Sosai ma kuwa ai karatu, ana yi saboda kar ka zauna a jahili ne.

Usman Sulaiman Mai Fata: Me zai hana idan ka jira gwamnati yunwa za ta kashe ka (Why not? If you seat and wait for Government you will die of hunger).

Murtala Naseer:  Allah Ya sa wa rayuwarka albarka da irinku za mu bai wa maras da kunya a Najeriyarmu ta Arewa.

Abubakar Safana: Shi ya fi komai sauki, kai dai nemi rufin asiri

Salihu Y. Alfa: Ko dankalin hausawa saida shi zan yi, wannan zamani fa ba na wasa ba ne.

Real Suleiman Abdullahi Awashaka: To me ye laifin ai kasuwanci ne, da in zauna talauci ya yi min katutu, da yawa wallahi gara na yi sana’a ko wace iri ce, idan zan rufa ma kaina asiri ba laifi ba ne. Allah Ya sa matasanmu su fito wajen neman halal su bar cima kwance.

Abdulkarim Musa Bida: To miye aibu a ciki, digiri kuma miye ce a wannan karni da muke ciki, mutun ya yi anfani da lafiyar da Allah Ya ba shi ya nemi kudi shi ne mafita.

Nafiu Maibulawus Karu: Idan ina da kwalin digiri ban iya kera komai ba ba ni da masana’anta tawa ta kaina to mai kera lauje da fartanya a kauye ya fi ni amfani ga al’umma.

Ibrahim Maman Ibrahim: Ni ko ina da digirin-digir-gir, zan iya sana’ar sayar da dankalin turawa, ko ba komai don na rufa wa kaina asiri.

Barham M Mu’azzam: To ai jahilci ne don ka yi karatun boko har ka samu digri ka ce sai ka samu aiki, wanda za ka zauna a ofis. Shi karatu yana taimaka maka ka san yadda za ka tafi da rayuwarka, amma ba dole ne sai gwamnati ta ba ka aiki ba.

Usman Lawan Tijjani: Sosai ma kuwa, to wai me kuka dauki digiri sai ka ce sai da shi za a shiga Aljanna.

Ahmad Muhhamad: Kasuwanci ke nan ALHAMDULILLAH, shi ya kamata mutum ya koya. In dai ni ne ba digiri ba ko shaidar digiri ta BSc ko digiri na biyu wato Masters din da ake cewa. Toh  insha ALLAHU zan sayar da dankali, kai har da albasa ma. ALLAH Ya kyauta.

Mustapha Ibrahim: Digirin banza! Duk Digirin da ya kai shekara goma ba tare da samun aiki ba, ai sunansa takardar kosai.

Ammar Suraj: To mene kwalin digirin, ai da ma don ka samu dabarun zaman duniya ya sa ake yin sa sannan mutum ya san waye shi a zamanance. Ni ma nawa digirin na hanya ban da dalilin annobar coronavirus. Amma sabgogina sun ishe ni.

Umar Sada: Ka gama digiri ba ka da sana’ar hannu. Lallai za ka gane dalilin da ya sa taken Najeriya ya kare da ‘So Help Me God’.

Sani Danladi: Ai ko ba aiki an kori jahilci kuma in har za ka iya samun rufin asiri ai an wuce wurin.