✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalliya ta biya kudin sabulu a mulkin Buhari – Sanata Abu Ibrahim

Sanata Abu Ibrahim tsohon dan Majalisar Dattawa ne mai wakiltar Katsina ta Kudu a zauren majalisar. A cikin wannan tattaunawar, ya yi bayani daki-daki kan…

Sanata Abu Ibrahim tsohon dan Majalisar Dattawa ne mai wakiltar Katsina ta Kudu a zauren majalisar.

A cikin wannan tattaunawar, ya yi bayani daki-daki kan nasarorin da Shugaba Buhari ya samu a tsawon shekaru biyar a kan karagar mulki, inda ya ce ya taka rawar gani.

Yaya za ka kwatanta shekaru biyar na mulkin Buhari?

Akwai tambayar da ba za ka iya amsa ta ita kadai ba tare da ka dan yi karatun baya ba. Kowa ya san irin badakala da barnan da gwamnatocin baya suka yi ta hanyar cin hanci da rashawa, wadaka da dukiyar al’umma da kuma dakile cigaban kasa.

Dukkanmu mun san irin kalubalen da wannan gwamnatin ta tarar a bangaren rashin tsaro, rashin ayyukan yi da kuma rashin ayyukan raya kasa.

Wadannan su ne abubuwan da gwamnatin ta yi ta kokarin gyarawa cikin wadannan shekaru biyar din.

Saboda haka, idan na kwatanta abin da Buhari ya cimma a shekaru biyar, la’akari abubuwan da gwamnatocin baya su ka yi, to tabbas zan ce ya ba mara da kunya kuma kwalliya ta biya kudin sabulu.

Idan kuma muka yi la’akari da rawar da yake takawa wajen cigaban kasa, to lallai zan iya cewa yana kan tafarki, ko da yake akwai abubuwan da ya kamata ya kara mayar da hankali a kai.

Wadanne abubuwa za ka bayyana a matsayin nasorori da kuma kalubalen wannan gwamnatin

Bayyana nasarorin wannan gwamnati ba wani abu ne mai wahala ba, abubuwa ne a zahiri ga su nan karara. Kafin zuwan wannan gwamnati a 2015, akwai matsalolin da kusan sun zame mana jiki a Najeriya.

Tun daga zuwan wannan gwamnatin muka daina fuskantar karancin mai lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara. A irin wadannan lokutan a da ‘yan bunburutu ne ke cin karen su babu babbaka.

Akwai lokutan da a baya jihohi ke gaza biyan ma’aikatansu albashi, da zuwan wannan gwamnati ta fara ba wa jihohi kudaden tallafi wannan matsalar ta zama tarihi.

Bugu da kari, irin yadda tsofaffin ‘yan fansho ke cincirindo a titunan Abuja don tuni ga gwamnati ta biya su hakkokinsu, shi ma yanzu ya zama tarihi.

A bangaren noma kuwa, a karon farko gwamnatin ta sami nasarar kawo karshen shigo da shinkafa. Yanzu Najeriya ta tsaya da kafarta wajen nomawa da kuma sarrafa shinkafa.

Nan ba da jimawa ba Insha Allahu za mu fara fitar da ita kasashen waje. Najeriya ta sami nasarar adana kusan Dala miliyan biyar a kullum sakamakon daina shigo da shinkafa da alkama.

A shekarar da ta gabata ta 2019 kawai alal misali, harkar noma ta tallafa da sama da sama da kaso 22.12 cikin dari na tattalin arzikin kasa, wannan ba karamin cigaba ba ne.

Ta bangaren tsaro kuwa, yau a Abuja da wasu sassan kasar da dama mutane na barci da ido biyu. Shekaru shida da su ka shude hakan ba ya samuwa.

Kungiyar Boko Haram sai da ta kusa mayar da yankin Arewa Maso Gabas karkashin ikonta, ta rika kai hare-hare kusan kowanne bangare na kasar har da Abuja.

Kungiyar da ke da tsaurin idon yin fito-na-fito a baya yanzu sai dai ta kai harin sari-ka-noke saboda yadda sojojin Najeriya ke ci gaba da ragargazar su.

Hakika ba zai yuwu a ce babu matsalar tsaro ba yanzu, amma a zahirin gaskiya ba za a kamatanta da shekarun baya ba.

Ko da yake an yi galaba kan Boko Haram amma akwai bukatar a kara hobbasa kan matsalar barayin shanu da masu garkuwa da mutane da ‘yan fashin daji a yankin Arewa Maso Yamma.

A bangaren ayyukan raya kasa kuwa, na san za ku yarda da ni cewa kasar ba ta taba samun cigaba irin wannan lokacin ba. Cigaba ba wai kawai ta fuskar girman ayyukan ba, a’a hatta yadda ake fitar da kudaden ma ya sha banban da yadda aka saba.

Ka duba farfado da harkar sufurin jiragen kasa, ginin manyan hanyoyi a dukkan shiyoyin siyasa guda shida, da kuma aikin ginin gadar Naija ta biyu wanda gwamnatocin baya suka yi ta karairayi a kai.

Hakazalika, akwai ayyukan samar da tashoshin wutar lantarki da kuma samar da wutar a wasu manyan kasuwanni da makarantu a fadin kasar nan; inganta samar da wutar, aikin tashar wutar ta Mambila wadda in aka kammala zai inganta megawatt din wutar a fadin kasa.

A karon farko a tarihin Najeriya, yanzu muna da nagartaccen tsarin tallafawa mara sa karfi.

A tarihin Najeriya, ka taba ganin an kai tsoffin gwamnnoni da wasu manyan jami’an gwamnati gidan kaso? Ba a taba samun haka ba a tarihi, amma da zuwan wannan gwamnatin mun ga hakan ta faru.

Yanzu ana yin komai babu boye-boye. Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC tana aikinta yadda ya kamata. A shekaru biyar din nan ta yi nasarar gurfanar da sama da mutane 1,500 bisa laifuffukan rashawa daban-daban.

Daga shekarun 2015 zuwa 2018 kawai, an sami nasarar kwato kimanin Naira biliyan 794, Dala miliyan 261, Yuro miliyan daya, da kuma katafarun gidaje sama da 407 daga hannun masu almundahana. Wannan fa bai ma kunshi na 2019 da kuma wadanda yanzu ake shari’a a kansu ba.

Tabbas mun san yadda ake yaki da cin hanci dole a samu tirjiya, amma za a dakile ta.

Yaya za ka bayyana salon mulkin Buhari? Wasu sun ce yana da rauni, wasu sun ce ba ma shi ke gudanar mulkin ba, wasu kuma suna kiran sa da ‘Baba Go Slow’.

Shugaban da ya san ya kamata ne kadai ke nada mutane a mukami kuma in dai ya aminta da nagartarsu ya bar su su gudanar da ayyukansu ba tare da katsa-landan ba.

Ni ba na ganin wannan a matsayin rauni, hasali ma ni a nagarta nake kallonshi da ba kowane shugaba ake samu da ita ba.

Shin da gaske ne Buharin ba shi da kazar-kazar da har ya cancanci a kira shi da Baba Go Slow?

Ko daya! A cikin wadannan shekaru biyar din babu wata gwamnati a baya da ta iya cimma nasarar da gwamnatin Buhari ta samu kuma take cigaba da samu, duk da matsalar kudaden shiga da kasar ta fuskanta sakamakon karyewar farashin danyen mai a kasuwar duniya.

An ce Buhari ba shi da kazar-kazar, amma ga shi gadar Naija ta biyu da PDP ta gaza yi cikin shekaru 16 an kusa kammalawa. Ko daya, sam mulkin Buhari ba ya tafiyar hawainiya.

Ana zargin yawanci mukaman da shugaban yake rabawa ya fi ba ‘yan arewa, me za ka ce kan haka?

Wannan zargi ne da ba shi da tushe ballantana makama. Zargi ne na ‘yan adawa, kuma a zahirin gaskiya, alkaluma suna nuna akasin hakan.

A yanzu haka, yankin Kudancin Najeriya na da kaso 52 cikin dari in an kwatanta da kaso 48 cikin dari da yankin Arewa ya samu tun da wannan gwamnatin ta zo. Duk mai tantama ya je ya bincika daga hukumar raba-daidai ta kasa ba wai aiki da jita-jita ba.

Misali, an sha fada wa mutane cewa ragamar tsaron kasa tana hannun ‘yan arewa kacokam, amma a zahirin gaskiya ba haka bane. Baban Hafsan tsaro na kasa wanda shi ne kololuwar mukami a sojoji, Gabriel Olanisakin, dan kudu ne. Babban Hafsan sojojin kasa, TY Buratai dan jihar Borno ne, Babban Hafsan sojin Sama Sadique Abubakar dan Bauchi ne, yayin da Ibok-Ete Ekwe, Babban Hafsan sojin ruwa dan jihar Kuros Riba ne. To ta ina aka danne kudu.

Daga cikin manyan alkawuran wannan gwamnati kamar yadda bincikenmu ya gano daga cikin manufofin jam’iyyarku akwai samar da megawatt 20,000 na wutar lantarki, tabbatar da kudurin dokar man fetur (PIB), cire wa masu mulki rigar kariya, maye gurbin jihar mutum ta asali da jihar da yake da zama, fadada tattalin arzikin kasa, rage tsadar tafiyar da gwamnati da kuma gyara bangaren shari’a. Zuwa yaushe kuke sa ran cika wadannan alkawuran?

A 2015, Najeriya na samar da kasa da megawatt 3,900 na wutar lantarki, ko da yake injinanta suna da karfin samar da megawatt 7,445. A yau, Najeriya na samar da megawatt 4,678 kuma an ba kimanin kamfanoni 20 lasisin lalubo hanyoyin kara inganta samar da makamashin.

Sama da kamfanoni 20 kuma suna aiki a kashin kansu don samar da kimanin megawatt 10,000 nan da shekaru biyu masu zuwa.

Hakan kenan na nuna cewa in aka sami nasarar kammala aikin Mambila, hankoron da ake yi na samar da megawatt 20,000 zai iya tabbata nan da wani lokaci kankani, kafin wannan gwamnatin ta kammala wa’adinta.

Ta bangaren fadada tattalin arziki kuwa, labarin akwai dadin ji. Harkar noma yanzu haka tana samar da kashi 22.12 cikin dari na tattalin arziki, kasuwanci 15.61, harkar masana’antu kaso 11.64, ma’adinai 8.84, yayin da fasahar sadarwa ta samar da ksahi 11.64 a shekarar 2019.

Wasu masana da jaridar Daily Trust ta tattauna da su kan aiwatar da alkawuran jam’iyyarku sun bayyana rashin gamsuwa da abin da k ka cimma a shekaru biyar. Sun bayyana ku a matsayin jam’iyyar da ta gaza. Me za ka ce kan haka?

Bana tunananin akwai wani mutum da zai bayyana wannan gwamnatin a matsayin wadda ta gaza ko mai alkawuran karya sai ‘yan adawar siyasa. Wadannan kuma ba za mu hana su magana ba.

Shin aikin gadar Naija ta biyun ce karya ko batun habbaka noman shinkafa ko shirin N-power, Tradermoni, Marketmoni ko ciyar da ‘yan makaranta?

Shin aikin jiragen kasa ne karya ko batun yaki da cin hanci. Wadancan tsoffin gwamnonin da aka daure a wasan kwaikwayo ne ko kuwa kadarorin da aka kwato ne karya?

A tarihin kasar nan babu wata gwamnati da ta kudiri aniyar cire mutum miliyan 100 daga talauci sai tamu, kuma muna dab da cimma wannan burin.

 

Shin ya yanayin damuwar Shugaba Kasa ganin cewa manyan alkawuran da ya yi har yanzu bai kai ga cika su ba?

Babu wata damuwa tare da Buhari, kawai da yana nan ya yi tsayin daka wajen ganin ya cika wadannan alkawura nan da 2023.

Ko ‘yan adawa yau sun aminta da cewa shugaban na kan tafarkin cimma nasara kan muhimman alkawuransa ta fuskar tsaro, yaki da cin hanci da rashawa da kuma samar da ayyukan raya kasa.

 

Ta wadanne bangarori ne ka ke ganin wannan gwamnatin ta gaza?

Babu wata gwamnati a duniya da ba ta da kalubale ko kurakurai. A zahirin gaskiya zan so a ce Buhari ya kara matsa lamba wajen yaki da cin hanci, amma kash, mulkin dimukradiyya muke kuma komai akwai iyakarsa.



Me ‘yan Najeriya ya kamata su sa rai daga wannan gwamnatin bayan wucewar annobar coronavirus?

Baya ga kwamitin kar-ta-kwana da shugaban ya kafa na yaki da cutar da kuma hukumar NCDC, tuni gwamnatin ta kafa wani kwamiti da zai tsara farfado da harkar tattalin arzikin kasa bayan kawar da wannan cuta.

Mun sani sarai cewa babu kasar da tattalin arzikinta zai kasance kamar na da. Amma irin manufofin da gwamnati take tsarawa ‘yar manuniya ce kan halin da gobe za ta tsinci kanta a gobe.

Duk da cewa kusan samun kudade ta bangaren man fetur ya tsaya cik, amma ba abun da ya tsaya a kasar, har yanzu muna biyan ma’aikata albashinsu.

‘Yan Najeriya su tsammaci ganin dawowar tattalin arziki mai cike da karsashi. Sama da naira biliyan 50 gwamnati ta ware don tallafa wa masu kanana da matsakaitan sana’o’i. Sama da Naira biliyan 100 kuma aka ware wa masu harkar sarrafa magunguna.Da ma can sauran bangarorin masu zaman kansu za su ci gajiyar tallafin na gwamnati.

Koma dai me yake faruwa a wasu sassa na duniya, ‘yan Najeriya su sa ran ganin farfadowar tattalin arziki da zarar wannan annobar ta wuce.