✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake kwalliyar ‘aloe vera’ a fatar jiki

Barkanmu da sake haduwa da ku a wannan filin namu na kwalliya. Mata da dama na sha’awar fatarsu ta yi sumul musamman a ce babu…

Barkanmu da sake haduwa da ku a wannan filin namu na kwalliya.

Mata da dama na sha’awar fatarsu ta yi sumul musamman a ce babu Kuraje. Wannan ganyen na Dauke da sinadarai da dama wadanda sukan iya dada tsawon gashin mace da sanya fuska sheKi da gyaran jiki da sauransu.

Don haka ne a yau na kawo muku hanyoyin da za a bi don amfani da shi wajen gyaran fata da gashi.

Ina so masu karatu su gane cewa a duk rubutun da nake yi idan na lissafo ababen hadin kwalliya, guda daya daga cikin ababen nake so a yi amfani da shi. Domin yawan sanya wa fuska ababe da dama na haifar da fesowar kuraje.

Wadannan kuwa sun hada da:

  • Kodewar fuska: Yawan aiki ko shiga rana na sanya fuska ta yi baki ko launinta ya zama biyu.

A samu ganyen ‘aloe vera’ sannan a matse ruwansa sai a matsa ruwan lemun tsami a kwaba a riKa shafawa a fuska don gyaran irin wannan fata.

  • Yankwanewar Fata: Wannan ganye na rage shekaru daga fuskar mutum. A matse ruwansa sannan a hada da ruwan ‘Rose’ sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti 10 zuwa 15 kafin a wanke a kullum.
  • Domin fuska mai yawan gumi/maiko: A samu ganyen a dan kankare bayansa sannan a dora tukunya da ruwa har sai ya yi laushi sannan a sauke a zuba zuma bayan ya huce sannan a shafa a fuska na tsawon minti 20 a kullum kafin a shiga wanka.
  • Domin gautsin fata: A markada dabino da gurji sannan a matse ruwan ganyen ‘aloe vera’ da ruwan lemun tsami sannan a shafa a fuska da jiki na tsawon minti talatin kafin a wanke.
  • Gyaran gashi: A matse ruwan ‘aloe vera’ sannan a hada da man zaitun a kwaba da kyau sosai sannan a rika shafawa a fatar kai da saman gashin a duk lokacin da aka yi niyyar wanke gashin kai kafin a wanke. Yin hakan na sanya gashi ya yi baki da kuma dada masa tsawo da karfi.