✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamandojin soji sun yi ganawar sirri kan yanayin tsaron Najeriya

Kwamandojin Soji daga Hedikwatar Tsaro sun yi ganawar sirri kan hare-haren da aka kai wa cibiyoyin tsaro

Manyan Kwamandojin Soji daga Hedikwatar Tsaro ta Najeriya sun yi wata  ganawar sirri kan yanayin da tsaron da Najeriya ta ke ciki a baya-bayan nan.

Ba a gayyaci ’yan jarida ko sanar da su game da zaman ba, amma majiyarmu ta tsaro ta ce an yi zaman na ranar Laraba ne bayan hare-haren da aka kai wa wasu jami’an tsaro da cibiyoyin tsaro musamman a yankin Kudu maso Gabas.

Majiyarmu ta ce zaman da ya gudana a otel din Trancorp, ya tattauna kan hanyoyin dakile maharan, wadanda ake zargin ’yan kungiyar IPOB mai ikirarin fafutikar kafa kasar Biafra ne.

Ta ce kwamandojin sojin sun damu da yadda ake kai wa ofisoshin ’yan sanda hari, da kuma yiwuwar fara kai wa sansanonin soji  da ke yankin makamantan hare-haren.

“Hafsoshin sojin na daukar matakin dakile hare-hare ne, shi ya sa suka yi zaman domin dakile yiwuwar kai hare-hare a kan sansanonin soji a Kudu maso Gabas da wasu wurare kamar yadda aka kai wa Hedikwatar ’Yan Sandan Jihar Imo da gidan yari.

“Suna kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki na kasar kan yadda za su shawo kan matasa daga yankunan siyasan kasar cewa su guji biye wa bata-garin da ke aikata ta’asa a nan da can,” inji majiyar.

Aminiya ta tuntubi kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya Birgediya Mohammed Yerima domin jin karin bayani, amma ya ce, gayyatar su aka yi domin su halarci wani taro a otel din Transcorp.