Kwamishinan Bayelsa ya kubuta daga hannun masu garkuwa da shi | Aminiya

Kwamishinan Bayelsa ya kubuta daga hannun masu garkuwa da shi

    Bassey Willie, Yenagoa da Abubakar Muhammad Usman

Kwamishinan Harkokin Kasuwanci na Jihar wanda mahara suka sace, Mista Oparniola Otokito, ya kubuta bayan shafe kwana hudu a hannunsu.

Maharan sun shiga gidan kwamishinan da ke yankin Otuokpoti a Karamar Hukumar Ogbia a ranar Alhamis din da ta gabata, sannan suka yi awon gaba da shi.

Sakataren Yada Labaran Gamnan Jihar, Douye Diri, Mista Daniel Alabrah ne ya tabbatar da kubutar kwamishinan a yammacin ranar Litinin.

Mista Alabrah ya aike da sako ta dandalin WhatsApp cewar “An samu nasarar kubutar da Kwamishinan Kasuwanci da aka sace. Karin bayani na tafe,” kamar yadda ya wallafa.

A ranar Lahadi ne Gwamnan Jihar, Sanata Douye Diri ya sha alwashin kubutar da Kwamishinan cikin koshin lafiya daga hannun wanda suka sace shin.

Kazalika, Gwamnan ya kuduri aniyar gurfanar da duk wanda suke da hannu a sace Kwamishinan tare da maganin masu aikata miyagun laifuka a fadin Jihar.

Sai dai ya zuwa yanzu, Rundunar ’Yan Sandan Jihar ba ta ce komai ba kan lamarin, sannan kakakinta a Jihar, SP Asinim Butswat ba ya daukar waya bare a ji ta bakinsa.