✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamishinan da aka zarga da murnar mutuwa ya kamu da Coronavirus

Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji, wanda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tube saboda ya wallafa wasu kalamai a shafinsa na Facebook…

Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji, wanda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tube saboda ya wallafa wasu kalamai a shafinsa na Facebook game da mutuwar Abba Kyari, ya ce ya kamu da cutar coronavirus.

Injiniya Mu’azu ya wallafa wani sako a shafinsa na Facebook yana cewa an fitar da sakamakon gwajin da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta yi masa kuma ya nuna yana dauke da cutar.

Tsohon Kwamishinan ya ce yanzu haka yana daya daga cikin cibiyoyin killace masu dauke da cutar coronavirus da ke jihar Kano.

Injiniya Mu’azu Magaji ya fitar da sanarwar ne kamar haka:

“Da safen nan sakamakon gwajin da NCDC ta yi min ya fito… An tabbatar ina dauke da COVID-19… Kuma an kai ni daya daga cibiyoyin kula da masu dauke da cutar… A yi mana addu’a.”

Shafin Facebook na Injiniya Muazu Magaji

A watan Afrilu ne dai Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tube kwamishinan bayan da Injiniya Muazu Magaji ya wallafa wasu kalamai da galibin mutane a shafukan sada zumunta suka fahimci murna ce ta mutuwar shugaban ma’aikata a fadar shugaban kasa.

Wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai Mohammed Garba ya fitar ta ce furta irin kalaman da kwamishinan ya wallafa a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati laifi ne, “ya kamata ya kare martabar ofishinsa”.

“Gwamnatin Ganduje ba za ta lamunci irin wadannan kalaman daga wani jam’in jihar ba”, inji sanarwar.

Ba a fahimce ni ba, cewar Injiniya Mu’azu Magaji

Bayan sanar da tube Kwamishinan, Injiniya Mu’azu Magaji, ya ce shi bai yi murna da mutuwar Shugaban Ma’aikatan a Fadar Shugaban Kasa Malam Abba Kyari ba.

Da yake bayyana hakan a wata sanarwa, tsohon kwamishinan ya ce a matsayinsa na Musulmi kuma mai kishin Najeriya, wadanda suka zaci ya yi murna da mutuwar Malam Abba Kyari ne ba su fahimce shi ba.

“Na wallafa sakwanni da dama a Facebook din da kuma ta hannun mataimakana na musamman ina alhinin mutuwar Abba Kyari, amma babu wanda ya yaba ko ya yi ikirari cewa na yi.

A cewarsa, Malam Abba Kyari ya yi dace COVID-19 ta yi ajalinsa, saboda ya yi shahada kamar yadda karantarwar Musulunci ta nuna.

“Manzonmu (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya tabbatar mana da hanyoyin shahada a Sahihul Bukhari, Kitabul Jihad was Siyar.