✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamishinar Lafiyar Kaduna ta harbu da COVID-19

Cutar COVID-19 ta kama Kwamishinar Lafiya ta Jihar Kaduna, Amina Mohammed-Baloni. Kwaminishinar ta sanar da hakan ne ta shafinta na Twitter a ranar Juma’a  inda…

Cutar COVID-19 ta kama Kwamishinar Lafiya ta Jihar Kaduna, Amina Mohammed-Baloni.

Kwaminishinar ta sanar da hakan ne ta shafinta na Twitter a ranar Juma’a  inda ta ce tuni ta fara killace kanta domin samun kulawa.

“Bayan sanarwar da na samu cewa na kamu da cutar, na fara killace kaina yadda ya kamata.

“Ina fatar samun sauki cikin sauku da wuri, kuma ina rokon kowa ya bi matakan kare lafiya na COVID-19 da suka hada da sanya takunkumi a cikin jama’a; tsaftacce hannu a-kai-a-kai; da kuma guje wa shiga taron jama’a,” inji ta.