✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Kwanan nan za a yi dokar da za ta haramta cin ganda a Najeriya’

'Najeriya ce kadai kasar da ke cinye fatar dabbobi'

Cibiyar Bincike kan Kimiyya da Fasahar Fatar Dabbobi ta Najeriya (NILEST) da ke Zariya a jihar Kaduna, ta ce kwanan nan za ta kirkiro dokar da za ta haramta cin ganda a matsayin nama a Najeriya.

Shugaban cibiyar, Farfesa Muhammad Yakubu, wanda ya bayyana hakan ya kuma ce daukar matakin ya zama wajibi don a samu farfado da masana’antar fatar da take cikin masassara a halin yanzu.

Ya ce ya zama wajibi a kawo karshen dadadiyar al’adar nan ta cin ganda wacce a likitance ba ta kara wa jiki komai domin a bunkasa tattalin arzikin kasa.

Ya ce, “A iya sani na, a duk duniya ’yan Najeriya ne kawai da suke fifita ganda a matsayin abinci, alhalin ba ta da wani amfanin a likitance ga jiki.”

Shugaban ya ce cibiyar na hadin gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki domin shirya dokar domin su nufi Majalisar Dokoki ta Kasa don fito da dokar.

Ya kuma ce, “Akwai lokacin da aka gabatar da kudurin dokar a Majalisar Dokoki, har aka tafka muhawara a kai, amma ban san yadda aka yi batun ya sha ruwa ba.

Farfesa Muhammad Yakubu ya ce yawan cin gandar da ake yi shi ne babban kalubalen da masana’antar fata take fuskanta a Najeriya.

Ya ce, “Idan muka sa masana’antunmu na fata suka fara aiki yadda ya kamata, suna kera takalma da jakunkuna, zain yi wahala mutane su sami gandar da za su ci.” (NAN)