✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu ci gaba da rajistar masu zabe – INEC

Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta ce nan ba da jimawa ba za ta ci gaba da yin rijistar katin zabe wanda…

Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta ce nan ba da jimawa ba za ta ci gaba da yin rijistar katin zabe wanda ta dakatar a watannin baya saboda annobar COVID-19.

Kwamishinan hukumar a Jihar Kogi, Farfesa James Apam shi ne ya sanar da hakan a garin Onyadega na Karamar Hukumar Ibaji ta Jihar Kogi.

James wanda ke jawabi ga masu ruwa da tsaki kan shirye-shiryen zaben cike gurbin da za a yi a karamar hukumar ya ta’allaka tsaikon yin rajistar a yankin a kan annobar.

Ya kuma ba da tabbacin cewa zuwa farkon shekara mai zuwa za ci gaba da rajistar tare da kira ga wadanda ba za su samu damar kada kuri’a a zaben ba da su yi hakuri.

Ya ce zaben cike gurbin ya biyo bayan mutuwar dan majalisar da ke wakiltar yankin a Majalisar Dokokin jihar, Mista John Abah a watan Yuni.

Kwamishinan ya kuma ce INEC za ta samar da sinadaran tsaftace hannu, na’urar gwajin zafin jiki da kuma kiyaye sauran ka’idojin kariyar cutar.