✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwankwasiyya: Ana zargin Dangwani da zagon kasa

Rikici ya kunno kai a tsakanin mabiyan tafiyar siyasa ta Kwankwasiyya a Jihar Kano.

Rikicin cikin gida ya kunno kai a tsakanin mabiyan tafiyar siyasa ta Kwankwasiyya a Jihar Kano.

Bangarorin sun fara gugar zana ne bayan rabon kayan abincin azumi nai miliyoyin Naira da wani kusa a tafiyar ya yi wa ’yan jam’iyyarsu ta PDP a fadin Jihar.

Makusanci kuma hadimi ga jagoaran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wato Sanusi Surajo ya ce, ya ga wani bidiyo na yawo wanda a ciki wani ke zargin, Dokta Yunusa Adamu Dangwani kan yunkurin kawo rudani da rabuwar kan magoya bayan Kwankwasiyya.

Dangwani shi ne tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Kano kuma tsohon Kwamishinan Ruwa a lokacin mulkin Kwankwaso a Jihar.

Ana zarginsa da nema kawo rudanin ne da nufin kalubalantar Abba Kabir Yusuf saboda ba a ba shi damar yin takara ba a zaben 2019.

Sanusi Surajo ya yi magana da kurman baki cewa, “Babu wani dan takarar gwamna da za su karba idan ba Abba Kabir Yusuf ba, don haka a yi watsi da kiraye-kirayen, shi ma Dangwanin ya yi watsi da kudurin nasa ko kuma ya fice daga tafiyar.

“Ko Kwankwaso ba zai canza mana Abba ba, idan ba ka goyon bayan Abba, to abin da zai fi maka sauki [shi ne] ka fice daga tsarin ko kuma ka bar jam’iyyar.

“Abba ya samu dumbin magoya baya, mutane sun karbe shi, ba za mu canza shi ba duk da muna sane da ire-iren zagon kasa da ake yi wa Kwankwaso amma da izinin Allah ba za su ci galaba ba.

“Kwankwaso ya mara musu baya, shi ya mayar da su abun da suka zama a yau, irin wadannan mutane ko zabe ba sa iya ci a mazabarsu,” a cewar Sanusi.

Sunan Dangwani ya zama labari abun tattaunawa tun lokacin da ya fara rabon kayan abincin azumi ga ’yan jam’iyya mabiya Kwankwasiyya.

Yanzu haka yana kara samun goyon bayan shugabanni da mambobi Kwankwasiyya, wadanda tuni suka fara yi masa kiraye-kirayen ya fito takarar Gwamnan Kano.

Kawo yanzu dai bangaren Dangwani sun ki cewa komai kan zargin.