✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwankwasiyya kamar kungiyar asiri ce –Kwankwaso

Kwankwaso ya ce tafiyar Kwankwasiyya na kara samun tagomashi a kowane lokaci.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana tafiyar siyasar Kwankwasiyya da yake jagoranta da tamkar wata ‘kungiyar asiri ce’ saboda yadda take kara samun tagomashi a kowane lokaci.

Sanata Kwankwaso, wanda ya bayyana haka yayin hira ta musamman da gidan talabijin na Trust TV wanda Aminiya ta saurara. Ya kuma yi ikirarin cewa Kwankwasiyyar ita ce take jan ragamar siyasar jam’iyyu a Jihar Kano a yanzu.

Ya ce ’yan siyasar da suka yi fice da wadanda suke cikin tafiyar, lokaci na zuwa da dukkansu za su sake hadewa a karkashin inuwar Kwankwasiyyar “Saboda muna karfafa ta, sannan mun kafa tubalinmu tun daga tushe, wanda hakan yana sosa ran ’yan siyasa da dama.”

“Yadda muke aiki a tsarin Kwankwasiyya ya sha bamban sosai, saboda mun yi amanna da gina mutane.

Daga 1999 zuwa yanzu, babu mahalukin da zai ga adadin wadanda suka ci gajiyar tafiyar Kwankwasiyya, sai lokacin da zabe ya zo ne kadai za ka iya sanin adadin mutanen,” inji shi.

Tsohon Gwamnan, wanda ya ce Jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben Gwamnan Jihar Kano a 2019, inda ya kara da cewa saboda wasu dalilai na jam’iyyar da ma tafiyar Kwankwasiyyar suka yanke shawarar bin lamarin cikin ruwan sanyi.

Ya ce: “Abin da muke yi a yanzu shi ne sake daura damara sannan mu tabbatar duk wanda ya ci zabe a badi an ba shi kujerarsa.

“Haka kuma, ina mai tabbatar maka dan Kwankwsiyya zai yi nasara a zaben.”

Sai dai tsohon Gwamnan ya ja kunnen jam’iyyun PDP da APC cewa lallai ne su sake lale a tsaretsarensu yana mai cewa yadda manyan jam’iyyun siyasar biyu suke tafiyar da al’amuransu akwai bukatar gyara.

Kodayake Kwankwaso ya nuna cewa zuwa yanzu dai ba ya magana da kowa a Jam’iyyar APC kan yiwuwar sauya sheka zuwa jam’iyyar.

Sai dai ba zai fid da ran shiga sabon tsarin tafiyar siyasar nan da ake ta magana a kansa na raba-gardama (third force mobement’ ba, yana mai cewa komai na iya faruwa, saboda ya fara tuntuba game da batun.