✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwankwaso da jam’iyya mai kayan marmari a Najeriya

Kamar dai a 2018, yanzu ma lokaci yana neman ya kure.

Kusan shi fa Kwankwaso ya san samun mulki a 2023 zai yi masa wahala duk da dai magoya bayansa akwai dan-karen karfin hali.

A irin gogewa da yawan mabiyan da yake da su, matsayin da aka ba shi a APC ne ya yi masa kadan, da ya je PDP sai ya iske su ma duk ba su da niyyar gwabzawa da APC da kyau, sun sa son rai kuma sun raina karfin APC da na Kwankwaso.

PDP sun kama wasu tarkace saboda su na da baitul mali, abin da Kwankwaso bai da shi, a sakamakon murde zaben Kano a 2019.

Murde wa Abba Gida Gida zabe ya jawo wa Kwankwasiyya cikas na gaske; ya raba wa Kwankwaso hankali, ya tilasta shi shiga siyasar gida, ga kalubale na rashin mulki.

Idan har ba sha’awar zama dan kallo yake yi ba, zaman Kwankwaso a PDP a irin wannan yanayi ba ta da amfani.

A nan kusa, ba zai samu takara ba, ba zai amfana da komai ba, sai dai su amfana da shi.

Bayan gwamna, Kwankwaso ya rike duk wata babbar kujera ta tarayya, burinsa daya ne a Duniya.

Daga nan har zuwa bayan 2023, Kwankwasiyya ba ta cikin lissafin PDP face nemawa PDP kuri’un Yan Arewa a Kudu.

Hakan ta sa yake neman inda zai fito da kan shi. Kuskure ne a siyasa ka ce wai a zauna a yi hakuri, dan siyasa kullum cikin lissafin zabe na gaba yake yi, ga shekaru su na tafiya.

Kamar dai a 2018, yanzu ma lokaci yana neman ya kure.

Kafa sabuwar jamiyya yana da wahalar gaske. Wasu sun jarraba a baya, suka yi asarar makudan kudi, kuma ba a dace ba. Ina ragowar mafita? A hade da wata karamar jam’iyya kamar su PRP da masu kayan marmari.

Hakan ta sa Madugun Kwankwasiyya ya burma cikin NNPP, jam’iyyar nan mai alama ta kayan marmari. Inda matsalar ta ke ita ce a gida watau Kano.

Wasu Kwankwasawa sun ajiye mukamansu a APC, sun bi Kwankwaso zuwa PDP a zaben 2019, suka yi biyu-babu. Su na tsoron sake tsalle zuwa NNPP babbar caca ce mai wahalar bullewa.

A nan ne ‘Yan Kwankwasiyya suka shiga matsala; su tsaya a PDP, ba za a yarda da jar hularsu ba, su cire jar hula (su rabu da Kwankwaso), ba su da tasirin kirki a zabe a karon kansu.

Su koma APC? Kwamacalar can ta zarce ta PDP. Ko me zai faru dai, Kwankwaso zai nemi sa’a a zaben kasa a 2023.

Hakan babbar asara ce ga jam’iyyar PDP domin babu dan hamayya da zai iya tarar karfin gwamnatin APC irinsa.

Wadanda za su yi wa NNPP takara a Jihar Kano za su iya kasancewa matasa masu ilmi da jar hula.

Za su gwabza da ‘yan uwasu wadanda suka zauna a PDP ko bangaren Shekarau da wadanda su Gwaggo suka tsaida a gefe guda.

Wadannan rukuni ba su da gogewa sosai a siyasa irin abokan gabarsu, amma su na da farin jinin Kwankwaso.

PDP za ta zama ba ta da farin jini, sai dai tana tare da masu dukiya da fitattu. APC kuma tana da gwamnati, burbushin Buhari, tare da dimbin rikicin cikin gida.

A wasu jihohin Arewa, NNPP za ta tattara wadanda suka rasa madafa a PDP da APC, da mabiyar darikar jar hula. Kuma a halin yanzu, jama’a suna bukatar su raba kafafunsu.

Dalilin Kwankwaso na takara a 2023 shi ne ya fito da kan shi. Idan har ya samu kuri’u masu yawan gaske, dole PDP ta neme shi idan tana neman komawa kan mulki, ko kuma APC ta lallabe shi ya dawo domin gudun ya birkita mata lissafi.

Shi dai zai bata ruwa ne, ba dole kuma ya sha ba. Shi ya sa babu bukatar magoya bayansa su rika zagin PDP, APC da sauran yan siyasa, ba a san gobe ba.

Idan ka ce na-kusa da Madugunka sun ci amana da suka ki shiga NNPP, a baya ai sun rike amanar, kuma shi yanzu ya kara cin amanar PDP.

Idan ta yi wa NNPP kyau a 2023, to ta gyaru ga Kwankwaso, idan ba a dace ba, to ya shiga wani layi mara fita, zai rage nauyi.

Muddin NNPP ta ba da mamaki a irinsu Kano, Kaduna, Katsina, Bauchi, da sauransu, to manyan jam’iyyu za sake jawo Kwankwaso; Su hadu da gawurtattun yan siyasa, su hada karfi su yi takarar gaske a gaba.

Kokarin CPC a 2011 ne ta sa dole Bola Tinubu suka hakura, su ka yarda aka hade-kai, ba don sun yarda da Janar ba.

Daga tafiyar TNM, zuwa yanzu babu wasu tulin mutanen kirki daga fadin kasar nan da ke tare da Kwankwaso, sai wasu tsofaffin barayi da wadanda suka gagara tabukai a gwamnatin APC da wasu tarkace.

Akwai sauran aiki. Kafin Kwankwaso ya samu mulkin kasa, ya na bukatar karbuwa da kyau a ko ina, dole ya hada kai da ‘yan siyasan kirki a Kudu, ya nutsa waje da Arewacin Najeriya, ya nunawa Duniya matsayarsa a kan tattalin arziki, fasalin kasa, ilmi, tsaro, da sauransu.

Wannan kuma dai jan aiki ne, farin jini kadai ba zai ba ka shugabanci ba kamar yadda tarihi ya nuna!

Muhammad Malumfashi yana shafin Twitter @m_malumfashi