✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwankwaso da ma ba abokin tafiyar Shekarau ba ne a siyasa

Akwai wadanda sun san cewa ba inda za'a a siyasance tsakanin Kwankwaso da Shekarau a cikin jam’iyya daya.

In ban da fadar Bature cewa “A siyasa babu aboki ko makiyi na dindindin sai bukata ta dindindin.”

Daidai da rana daya wadanda suka san tarihin siyasar wannan jamhuriyar a Jihar Kano, babu wanda ya taba tsammanin a ’yan shekarun nan za a iya zama a inuwar siyasa daya a tsakanin tsofaffin gwamnonin jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Sanata Ibrahim Shekarau.

Sanata Shekarau na Jam’iyyar ANPP a wancan lokaci, shi ya kada Sanata Kwankwaso a zaben Gwamnan Jihar na shekarar 2003, lokacin da Sanata Kwankwaso ke neman komawa karo na biyu a jam’iyyarsa ta PDP.

Kafin Malam Shekarau ya nuna niyyarsa ta shiga siyasa da neman kujerar Gwamnan Jihar Kano a shekarar 2002, yana rike da mukamin Babban Sakatare ne a gwamnatin Kwankwaso.

A wancan lokaci Malam Shekarau ya yi ta fadi-tashi a cikin kungiyoyin addinin Musulunci a jihar, musamman don neman tabbatar da shari’ar Musulunci a jihar da yadda gadan-gadan ya nuna yana son tsayawa takarar Gwamnan jihar, wannan ta sa Gwamnatin Kwankwaso ta dora masa karan-tsana.

Gwamnatin ta yi kokarin ta hana Malam Shekarau halartar wadancan tarurruka, amma abu ya faskara.

Kai, har jami’anta ta tura zuwa wasu makarantun sakandaren jihar na tsohuwar Jihar Kano inda Shekarau ya yi shugabancinsu ko za a same shi da aikata wata ta’asa don a dakile niyyarsa, amma ba a same shi ba.

Wannan karan-tsana, ta sa ala tilas, Malam Shekarau ajiye aiki ya tsunduma cikin siyasa da niyyar neman takarar Gwamnan Jihar.

Koda Malam Shekarau ya ajiye aikin gwamnatin Kwankwaso kiri-da-muzu, ta hana a biya shi kudadensa na barin aiki. Sai da Malam Shekarau zama gwamnan jihar a zaben shekarar 2003, aka biya shi.

Shi ma Sanata Shekarau a zamaninsa ya binciki gwamnatin Sanata Kwankwaso, sakamakon binciken ne ya dakile niyyar Sanata Kwankwaso ta sake tsayawa takarar Gwamnan jihar a zaben shekarar 2007, sai da Kotun Koli ta wanke shi, kana ya sake takarar a shekarar 2011, ya kuma yi nasara, bayan Malam Shekarau ya kammala wa’adin zangonsa na biyu.

Narkewar jam’iyyun APP ta su Malam Shekarau da wani bangare na PDP ta su Sanata Kwankwaso da na APGA da CPC ta Shugaba Buhari da ACN ta tsohon Gwamnan Jihar Legas yanzu dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar APC, Alhaji Bola Ahmed Tinubu, don kafa Jam’iyyar APC a shekarar 2013, ta sake ta da sabanin siyasar da ke tsakanin Sanata Kwankwaso da Sanata Ibrahim Shekarau.

Bayan kafuwar Jam’iyyar APC, sai tsarin mulkinta ya tanadi cewa Gwamna a jiha shi ne jagoran jam’iyya, don haka Gwamna Kwankwaso ne jagoran APC a Jihar Kano.

Wannan tanadi ya sa Malam Shekarau ganin gagarumar gudunmawa da ya ba da wajen kafa Jam’iyyar APC ya ce ba a yi masu adalci ba, don haka ba su ga wurin zama ba.

Sai Malam Shekarau da magoya bayansa suka canja sheka zuwa Jam’iyyar PDP, hakan ta sa tsohon Shugaban Kasa Dokta Goodluck Jonathan ya yi masa Minista.

Karatowar zaben shekarar 2019, bayan an karya kara a tsakanin Sanata Kwankwaso da ya tafi Majalisar Dattawa a jam’iyyarsu ta APC a zaben shekarar 2015, da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya gaje shi, sai Sanata Kwankwaso ya canja sheka daga Jam’iyyar APC, ya sake dawowa jam’iyyarsa ta asali wato PDP.

Hakan ya ba da dama Malam Ibrahim Shekarau da magoya bayansa suka sake canja sheka daga PDP zuwa APC.

A Jam’iyyar APC Malam Shekarau ya samu zama Sanatan Kano ta Tsakiya a zaben shekarar 2019.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya gayyato shi daga PDP zuwa APC, shi kuma ya sake nasara a zabensa zango na biyu.

Fara zabubbukan shugabanni da daliget na mazabu da kananan hukumomi da jiha da kasa baki daya a bara zuwa bana a Jam’iyyar APC, sai wata rigimar siyasa ta kaure a tsakanin wadansu wakilan majalisun dokoki na kasa daga jihar su shida a Jam’iyyar APC da kuma mai ba Gwamnan Jihar, Shawara kan Harkokin Siyasa Alhaji Ahmadu Haruna Zago a karkashin jagorancin Sanata Shekarau da ake wa lakabi da ’Yan Bakwai (G7) da bangaren Gwamna Ganduje.

Bangaren G7, ya zargi bangaren Gwamna Ganduje da yin watsi da sua gudanar da harkokin jam’iyyar a jihar, al’amarin da ya sa suka zabi nasu shugabanni da daliget, tun daga mazabu zuwa kananan hukumomi zuwa jiha zuwa kasa.

Karshe dai Kotun Koli ta halatta shugabannin APC na bangaren Gwamna Ganduje hakan ya kawo karshen wancan rikici.

Bayan hukuncin Kotun Kolin ne gayyar G7, ta watse kowa ya kama gabansa don nema wa kansa makoma, kasancewar da ma duk don zaben badi ake haka.

A wannan yanayi ne Sanata Shekarau ya zama bazawarar da kowa ke so ya aure a tsakanin Sanata Kwankwaso jagora kuma dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar NNPP da Gwamna Ganduje.

Bisa ga shawarar kwamitinsa na Shura, Sanata Shekarau da magoya bayansa suka canja sheka daga Jam’iyyar APC zuwa sabuwar Jam’iyyar NNPP, bisa ga abin da suka kira ba a yi masu adalci a cikin APC.

Bayan komawar su Sanata Shekarau cikin NNPP yau wata uku, can din ma sai suka zargi Sanata Kwankwaso da rashin yi masu adalci, kasancewar ya kasa cika masu alkawarin da ya yi masu na ba su wasu mukamai, in ban da takarar Sanata da aka ba Malam Shekarau, wanda dama yana kanta.

Sanata Kwankwaso a hirarsa da BBC, ya ce abin da ya sa ba a ba su mukaman ba shi ne saboda sun makara, amma in suka hakura an kafa gwamnati akwai mukaman da za a ba su.

Mai karatu in gajarce maka labari wannan shi takaitaccen tarihin siyasar Sanata Kwankwaso da Gwamna Ganduje a gefe daya kuma da Sanata Shekarau.

Yanzu dai maganar da ake dan takarar Shugaban Kasa kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP, jam’iyyar da aka dade ana rade-radin Sanata Shekarau da magoya bayansa za su koma, a ranar Lahadin wannan makon ya sauka Kano don ganawa da magoya baya da sauran masu ruwa-da-tsaki na jam’iyyarsu ta PDP, har tsawon kwana biyu.

A kuma ranar Litinin kuma a gidan Sanata Shekarau a wani kasaitaccen taron da aka shirya don karbar bakuncin Alhaji Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan Jam’iyyar PDP na kasa baki daya a karkashin jagorancin Shugaban Kwamitin Amintattun Jam’iyyar, Alhaji Walid Jibrin da Shugaban Jam’iyyar na Kasa Dokta Iyorchia Ayu, Sanata Shekarau ya bayyana fitarsa daga NNPP zuwa PDP, tare da janye takararsa ta Sanata a Jam’iyyar NNPP.

Dama can wadansu mutanen Jihar Kano sun san cewa ba inda za a siyasance tsakanin Sanata Kwankwaso da Sanata Shekarau a cikin jam’iyya daya.