✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwara United ta sayo dan wasan Brazil, Alves

Kungiyar Kwara United ta sayo dan wasan bayan Brazil, Lucas Ribeiro Alves, inda ya sanya hannu a kwantiragin shekara daya a matsayin aro. Manajan dan…

Kungiyar Kwara United ta sayo dan wasan bayan Brazil, Lucas Ribeiro Alves, inda ya sanya hannu a kwantiragin shekara daya a matsayin aro.

Manajan dan wasan, wanda dan Najeriya ne mazaunin Girka, Peter Danise Alade wanda shi ne shugaban kamfanin hada-hadar ’yan wasa na Prime Sports Management ne ya bayyana wa jaridar Punch hakan, inda ya ce dan wasan zai kawo kwarewa sosai.

Kwara United ta kuma sayo tsohon golan Najeriya, Dele Ayenugba daga kungiyar Hapoel Afula ta Isra’ila.

Da yake bayyana shirinsa na dawowa Najeriya da taka leda, Alves ya ce, “a shirye nake in buga gasar Firimiyar Najeriya.

“Bayan na bar Amurka saboda annobar coronavirus, sai na koma gida Brazil; Ina can ne sai Peter ya kirani cewa in zo in buga kwallo a Najeriya, inda ya bayyana min cewa ana buga kwallo da kyau.

“Hakan ya sa na amince na zo zan koyi abubuwa da yawa a nan. Abincin da yanayin abubuwa da yawa sun zama min sababbi, amma na ji matukar dadin yadda aka tarbe ni.”

Dan wasan mai shekara 25 ya buga wa kungiyar Corinthians ta Brazil, sannan ya yi wasa Amurka da sauransu.