✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwararowar makamai: Sojoji na so a gina ganuwa a kan iyakokin Najeriya

Sojojin sun ce hakan ne kawai zai magance matsalar kwararowar makaman.

Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gina manyan ganuwoyi a dukkan iyakokin Najeriya don magance matsalar kwararowar makamai.

Kwamanda Jemima Malafa, wacce ta wakilci rundunar ce ta bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa kan wasu kudurori a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai a Abuja ranar Litinin.

A cewarta, “Ya kamata mu gina ganuwoyi a tsakanin kasarmu da makwabtan kasashe.

“Ko a kwanan nan na je kasar Chadi, kuma na gano cewa akasarin kasashen da suka zagaye mu basu da wata kariya, shi ya sa yawancin mutanensu suke samun makamai cikin sauki kuma su sayar da su don samun kudade.

“Amma na fi zargin kasashen waje da suke sakin makamai sakaka ba tare da la’akari da hannun wadanda za su fada ba.

“Dalilin kenan da ya sa Najeriya ta shiga halin ni-’ya-su, kuma makamai ke shigo wa kasar cikin sauki,” inji ta.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa daga cikin kudurori guda hudun da ake kokarin amincewa da su don zama doka har da na neman kafa Hukumar Kula da Yaduwar Kanana da Matsakaitan Makamai ta Kasa.

Sauran sun hada da dokar takaita amfani da abubuwan fashewa, da ta neman amincewa a yi amfani da kyamarar sirri ta CCTV wajen tsaron kasa.

Kudurin karshe kuma na neman a kebe watan Nuwamba a matsayin wata na musamman don jinjina ga jami’an tsaro a Najeriya. (NAN)