✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta kama kayayyakin fasa-kwauri na N232m a Adamawa da Taraba

Kwastam ta kama haramtattun kayayyakin a akan iyakar ruwa.

Jami’an Hukumar Kwastam sun cafke wasu kayayyakin da aka yi fasa-kwaurin da kudinsu ya kai Naira miliyan 232 a jihohin Adamawa da Taraba.

Kwanturolan hukumar mai kula da jihohin biyu, Isiaka Ganiyu ne, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Yola.

Ya ce masu fasa-kwaurin na amfani da matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas wajen shigo da haramtattun kayayyaki.

Shinkafar waje da takin urea da ’yan ta’addan Boko Haram ke amfani da su wajen kera bam na daga cikin haramtattun kayayyakin da hukumar kwastam din ta kama.

Duk da tashe-tashen hankula a yankin Arewa maso Gabas, jami’an hukumar kwastam sun yi kokarin gane dabarunsu, inda suka dakatar da ayyukan masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Ya kuma ce kokarin da jami’an kwastam suka yi ya haifar da sakamako mai kyau bayan kama wasu haramtattun kayayyaki da suka kai Naira miliyan 232 a kan iyakar ruwa ta jihar Adamawa da Taraba.

Kwanturolan ya ce jami’ansa za su ci gaba da aiki ba dare ba rana domin dakile ayyukan masu fasa-kwaurin.

Isiaka Ganiyu ya kuma gargadi masu fasa-kwauri, inda ya yi alkawarin cewa duk za su fuskanci hukunci idan suka shiga hannu.

Kayayyakin da aka kwace sun hada da: takin Urea kilogiram 50 buhu 4,649, katan 1,500 na haramtacciyar kwayar Tiramol, shinkafa ’yar kasar waje da kayayyaki masu tarin yawa.